Nijar ta yanke wa ofishin jakadancin Faransa ruwa da wuta

Matakin na zuwa ne bayan cikar wa’adin korar jakadan kasar a Yamai

Nijar ta yanke wa ofishin jakadancin Faransa ruwa da wuta

Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron

Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar Nijar sun yanke wutar lantarki da ruwa a ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai, babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Turkiyya, Anadolu, ya rawaito cewa sojojin sun kuma hana a kai abinci ofishin, kamar yadda ya ambato majiyoyi da dama a kafafen sada zumunta.

Rahotanni sun ce sojojin sun kuma dauki irin wannan matakin a kan ofisoshin kasar da ke garuruwan Zinder da Tera da Oualam da Ayorou da Dosso da Yamai da Filingue da kuma a dukkan fadin kasar.

Shugaban kungiyar magoya bayan sojojin da suka yi juyin mulkin (CNSP), Alhaji Issa Hasoumi Boureima, ya bukaci dukkan masu hulda da ofishin da su yanke wuta da ruwa sannan kada wani ya kai musu abinci.

“Muna kira ga kamfanonin wuta da ruwa na NIGELEC da SPEN da su yanke wuta da ruwa a ofisoshin jakadancin Faransa da ke Zinder da Yamai,” kamar yadda aka ambato shi yana cewa.

Bugu da kari, kungiyar ta yi gargadin cewa daga yanzu, duk wanda ya ci gaba da samar musu da wadannan ababen, za ta dauke shi a matsayin makiyin al’ummar kasar.

Gargadin na zuwa ne bayan wa’adin kwana biyu da Nijar ta ba jakadan Faransa, Silvain Itte, ya fice daga kasarta ya cika ranar Lahadi.

Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin gwamnatin sojin ta Jamhuriyar Nijar da Faransa da ma kungiyoyi irin su ECOWAS, tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

To sai dai tuni Faransar ta mayar da martani inda ta ce sojojin ba su isa su korar mata jakada ba, tun da gwamnatinsu haramtacciya ce.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta