Nijar ta zartar da sabuwar dokar sanya ido kan addinai
Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince da wata sabuwar doka da ke bayyana yadda ake gina wuraren ibada a kasar, duk da cewa wadansu ’yan majalisa suna yin dari-dari da daftarin dokar. An dai kada kuri’ar amincewa da ita ce kwana biyu bayan wata tarzoma da aka yi a garin Maradi tare da kona wata […]
Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince da wata sabuwar doka da ke bayyana yadda ake gina wuraren ibada a kasar, duk da cewa wadansu ’yan majalisa suna yin dari-dari da daftarin dokar. An dai kada kuri’ar amincewa da ita ce kwana biyu bayan wata tarzoma da aka yi a garin Maradi tare da kona wata majami’a.
Wannan dai doka ce mai kunshe da ayoyi 21, kuma abu na farko ta tanadi bai wa kowa damar yin addininsa ba tare da wata tsangwama ba, tare da karfafa zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai mabambanta.
Har ila yau dokar ta yi bayani filla-filla dangane da abin da ake kira wuraren ibada, kuma wannan ne karo na farko da kasar ta samar da doka da ke bayyana hakan karara.
Dokar ta yi bayani game da yadda ake gina wuraren ibada, tare da bai wa gwamnati damar kara sa ido game da inda kungiyoyi ko kuma jama’a ke samun kudaden da suke amfani da su domin gina wuraren ibada a cikin kasar.
A karkashin dokar, ba wanda ke da izinin bude wurin ibada ko kuma koyar da addini sai da amincewar gwamnati, sannan kuma wani bangare na dokar ya bai wa kowane addini damar samun wakilci a Majalisar Kasa mai kula da Harkokin Addini.
Kafin wannan doka dai, akwai wani tsari, da ke sa ido kan lamuran da suka shafi Addinin Musulunci ne kawai a kasar.