Nijar: Za mu dawo da Bazoum ta ko halin-ƙaƙa —Sojojin ECOWAS

Kungiyar AU ta samu rabuwar kai kan matakin da za ta dauka kan masu juyin mulkin Nijar

Nijar: Za mu dawo da Bazoum ta ko halin-ƙaƙa —Sojojin ECOWAS

Sojojin Senegal a taron shugabannin ECOWAS kan juyin mulkin Nijar Abuja, rana 10 da Agusta, 2023. (Hoto by KOLA SULAIMON /AFP)

Manyan hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS sun ce kungiyar za ta dawo da mulkin farar hula a Jamhuriyar Nijar ta ko wace hanya.

Kungiyar ECOWAS ta ce akasarin kasashenta a shirye suke su tura sojojinsu a runduna a musamman da za ta murkushe juyin mulkin watan jiyada sojoji suka yi a Nijar.

A yayin taron manyan hafshoshin da ke gudana a birnin Accra na kasar Ghana, Kwamishinan ECOWAS, Abdel-Fatau Musah, Daukacin kasashen kungiyar  — in banda wadanda ke karkashin mulkin sojojin da suka yi mulki da kuma Cape Verde — sun shirya tura sojojinsu zuwa Nijar.

Shi ma a jawabinsa na bude taron manyan hafsoshin na ranar Alhamis, kwamishinan tsaro da zaman lafiya, Abdul Fatau Musah ya ce abin da ke gabansu shi ne ganin an dawo da mulkin farar hula a kasar.

Taron dai shi ne na biyu da manyan hafsoshin tsaron ke gudanarwa kan matakan da ya dace ECOWAS ta dauka wajen amfani da karfi a kan sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar.

Shugabannin kasashensu sun umarce su da su yi nazari da kuma ba da shawara a kan matakan da ya dace a dauka idan bukatar amfani da karfin soji ta taso, sakamakon bijirewar sojojin da suka yi juyin mulkin.

Sai dai kuma sojojin da ke mulkin kasashen Mali da Burkina Faso da Guinea Bussau, sun yi wa takwarorinsu na Nijar alkawarin taimako da yaki duk kasar da ta nemi kutsawa Nijar.

Masu juyin mulkin na Nijar kuma suka lashi takobin ragargaza duk kasar da ta nemi yin shisshigi a kasarsu, inda suka yi watsi da takunkumin karya tattalin arizikin da ECOWAS ta kakaba musu da cewa haramtacce ne da kuma rashi imani.

Shirin ECOWAS na amfani da karfin soji na ci gaba da fuskantar adawa daga wasu kasashe da kuma kungiyoyin jama’a ciki har da kasashen Amurka da Rasha wadanda ke bukatar ci gaba da daukar matakan diflomasiya domin warware matsalar.

Rahotanni sun ce taron kungiyar kasashen Afirka ta AU a kan juyin mulkin na Nijar bai kai ga daukar matsayin bai-daya ba, sakamakon rarrabuwar kawunan da aka samu tsakani kasashen da suka halarci taron.

Fira ministan da sojojin Nijar suka nada, Ali Lamine Zeine ya ce tuni suka fara shirin mayar da mulki a kasar, yayin da majiyoyi da dama ke cewa sojojin sun bayyana bukatar tattaunawa da kungiyar ECOWAS.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa