Nijeriya ba za ta ruguje ba a shekarar 2015 -Gwamnatin Amurka
Gwamnatin Amurka ta ce babu alamun da suke nuna cewa Najeriya za ta ruguje kafin zaben watan Fabarairu ko kuma bayansa. Jakadan Amurka a Najeriya, Mista James Entwistle shi ne yayin furucin yayin da yake ganawa da manema labarai a jihar Legas kan taimakon jirgin ruwan yaki da kasarsa ta baiwa Najeriya.Ya bayyana cewa duk […]
Gwamnatin Amurka ta ce babu alamun da suke nuna cewa Najeriya za ta ruguje kafin zaben watan Fabarairu ko kuma bayansa.
Jakadan Amurka a Najeriya, Mista James Entwistle shi ne yayin furucin yayin da yake ganawa da manema labarai a jihar Legas kan taimakon jirgin ruwan yaki da kasarsa ta baiwa Najeriya.
Ya bayyana cewa duk da cewa Najeriya tana fuskantar ‘babban kalubale’ amma alamu sun nuna kasar za ta jurewa matsalolin da take fuskanta.
Saboda haka ya ce ya kamata mutanen Najeriya su yi watsi da maganar da wasu ke yi na cewa kasar za ta ruguje a shekarar 2015.
Mista Entwistle ya ce ‘An sha tambayata a kan rugujewar Najeriya a shekarar 2015 amma da na koma na bincika sai na gano cewa babu wani rahoton gwamnati da ya nuna cewa Najeriya za ta ruguje a shekarar 2015. Ta yi wu wasu ko wani da ba jami’in gwamnati ba ya fadi haka amma ba ni da masaniya. A ganina kuma a matsayina na jakadan Amurka a wannan kasa ba na jin wani dar cewa Najeriya za ta ruguje a shekarar 2015. Shin mun ga wani alamu da ya nuna cewa Najeriya za ta ruguje? Ban san abin da kuke tunani ba amma ni ban ga irin wadannan alamu ba’ In ji shi
Ya ci gaba da cewa ‘Amma na ga alamun bunkasa wadanda suka fi karfin kalubalen da kuke da shi. A wannan rayuwa za ku cigaba da bunkasa kuma na hango kyakkawar makoma ga Najeriya’.
A ganinsa muddin gwamnatin tarayya ta yi abin da ake bukata a bangaren tsaro da cin hanci da makamantan su babu shakka makomar Najeriya za ta yi kyau.
Ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewa wai shugaba Barrack Obama ya sanya takunkumi a kan makaman Najeriya saboda rahotannin da suka nuna cewa Amurka ta ki sayar wa da Najeriya jirgin yaki mai saukar Ungulu mai suna kobra.
A kan haka sai ya bayar da hujjar cewa Amurka ta na kafffa-kaffa ne bias la’akari da ’yancin dan adam a kasar.
Ya bayyana cewa ofishin jakadancin Amurka a Najeriya yana tattaunawa dangane da wadansu makamai da kananan jiragen yaki don tallafa wa sojojin Najeriya.
Dangane da girmama ’yancin dan adam da kuma yaki da ta’addanci ya ce ‘Wasu na zargin mu a kan cewa ba mu damu da yaki da ta’addanci ba sai dai ’yancin dan adam. Abin da zan mayar da martani shi ne ni ban yarda da haka ba saboda dole ka yi abubuwa biyun a lokaci guda. A lokacin da kake yaki da ta’addanci dole a lokaci daya kuma ka kare ’yan cin jama’a. Mun gano cewa muddin ka rasa goyon bayan jama’a ka rasa komai. Amurka da Najeriya mun tattauna a kan haka kuma horon soja da muke bayarwa na shekaru an tsara shi ne ta wannan alkibla’.