‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’
Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Venezuela na cikin ƙasashen da aka fi tafka rashawa a duniya.
![‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’ ‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2020/08/wp-content_uploads_2018_06_bribery.jpg)
Nijeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024 a cewar ƙungiyar Transparency International.
A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa.
- BUA ya raba wa asibitoci magunguna a Sakkwato
- Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya suya sheka daga PDP zuwa APC
Alƙaluman ƙasashe mafi cin hanci da rashawa a duniya ya nuna yadda Nijeriya ta koma matsayin ta 140 daga ta 145 da take a baya a sahun ƙasashe 180 mafiya cin hanci da rashawa a duniya
Rahoton wanda ya yi nazari kan ƙasashen ya yi amfani da masana da ’yan kasuwa wajen tantance matsayin kowace ƙasa.
Ma’aunin tantance munin cin hancin ya kama ne daga maki sifili zuwa 100, inda sifili ke nufin mummunan matsalar cin hanci yayin da 100 ke nufin rashin matsalar baki ɗaya.
Rahoton ya yi la’akari ne da ƙarfin hukumomi a ƙasashen, da inganci zaɓe da kuma ɗabi’ar gwamnati.
Transparency International ta ce Nijeriya tare da wasu ƙasashe kamar Uganda, Mexico, Madagascar, Iraq da Kamaru sun samu maki 26 ne cikin 100.
Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Venezuela na cikin ƙasashen da aka fi tafka rashawa a duniya.
Transparency ta ce cin hanci babban barazana ce ga sauyin yanayi. Ta ce hakan yana kawo cikas wajen batun rage fitar da gurɓataccen iska da masana’antu ke yi.
Shugaban ƙungiyar François Valérian ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin mummunar matsala mai haɗarin gaske ga duniya.
Ya ce, duk da cewa wasu ƙasashe sun yi hoɓɓasa wajen murmurewa daga matsalolin na cin hanci da Rashawa amma har yanzu wasu na cigaba da ganin ta’azzarar matsalar.
Ƙungiyar ta ce daga shekarar 2012 akwai ƙasashe 32 cikin 180 da suka yi ƙoƙarin rage matsalar ta cin hanci da rashawa kodayake 148 daga ciki ko dai suna inda suke ko kuma matsalar ta ta’azzara.
Transparency International ta ce har yanzu ƙasashe 43 basu sauya daga matakin da suke tsawon shekaru ba.
A cewar ƙungiyar, akwai biliyoyin mutane da ke rayuwa a ƙasashen da rashawa ke ci gaba da illata rayukan jama’a a wani yanayi da take haƙƙin ɗan adam ke kaiwa ƙololuwa a irin ƙasashen.
François Valérian ya buƙaci ƙasashe su miƙe tsaye wajen yaƙar matsalar ta rashawa wadda ya ce babbar barazana ce ga ci gaban demokraɗiyya da taɓarɓarewar tsaro baya ga ta’azzara take haƙƙin ɗan adam.
A shekarar 2019 Nijeriya ta koma ta 146 bayan samun maki 26 yayinda ta koma ta 154 a 2021 bayan samun maki 24, inda ta koma ta 145 a 2023 bayan samun maki 25 gabanin komawa ta 140 a bana bayan samun maki 26.