Nijeriya ce hedikwatar talauci da yunwa a duniya — Obi
Kwatanta ƙalubalen da muke fuskanta da sauran ƙasashe ba zai magance matsalolin ba.
Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, kuma ɗan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana Najeriya a matsayin hedikwatar talauci da yunwa da rashin tsaro ta duniya.
A baya-bayan nan Obi ya sha bayyana ra’ayinsa kan mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda yake zargin yana tafka kura-kurai a manufofinsa da kuma mayar da hankali musamman a lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tattalin arziki.
- Ya kashe Naira miliyan 200 don zanen tattoo a jikinsa
- Ba za mu fitar da Aminu Bayero daga Fadar Nassarawa ba — ’Yan sanda
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X (wanda aka fi sani da Twitter), Peter Obi ya bayyana takaicin yadda masu riƙe da madafun iko suka yi watsi da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta da tamkar “ba mu muka fi kowa fama da talauci da yunwa ba.
“Mu ne hedikwatar talauci a duniya, kuma mun kasance cikin sahun mutanen da suka fi fama da rashin tsaro da yunwa a duniya.
“Mu ne a sahun gaba a fannin rashin ingantaccen ilimi da kuma mafi yawan yaran da ba su zuwa makaranta da yawan mace-macen jarirai da cin hanci da rashawa da rashin aikin yi.
“Haka kuma mu ne muka fi kowa a fannin rashin ababen more rayuwa da ƙalubalen kiwon lafiya da girman giɓin samun kuɗin shiga tsakanin talakawa da masu hannu da shuni, wanda yake babban ginshiƙi na cin hanci da rashawa…”
Obi, ya buƙaci shugabanin da su samar da ingantattun hanyoyin warware matsalolin da kuma hangen nesa don tinkarar ƙalubalen ƙasar, yana mai cewa kwatanta ƙalubalen da muke fuskanta da sauran ƙasashe ba zai magance matsalolin ba.