Nijeriya ta dakatar da Osimhen daga tawagar Super Eagles

An samu taƙaddama tsakanin Osimhen da Finidi George saboda ƙin sanya shi a wasu wasanni Super Eagles a bayan nan.

Nijeriya ta dakatar da Osimhen daga tawagar Super Eagles

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya NFF ta dakatar da ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles, Victor Osimhen.

NFF ta sha alwashin hukunta ɗan wasan ne har sai ya bayar da haƙuri kan wani faifan bidiyo da ya wallafa na caccakar tsohon kocin Nijeriya Finidi George da ya ajiye aiki a bayan nan.

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ɗaya daga cikin manyan mambobin da ke lura da sha’anin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya ya fitar a Yammacin wannan Larabar.

Sanarwar ta ce Osimhen ya ƙetara iyaka kuma hukumar ba za ta lamunci hakan ba, tana mai fatan wannan hukunci ya zama izina ga sauran ’yan wasan.

An dai samu taƙaddama tsakanin Osimhen da Finidi George tun bayan da kocin ya ƙi sanya shi a wasannin da tawagar Super Eagles ta yi a baya-bayan nan.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji