Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS

Nijeriya ta kasance ƙasa ta tara da ta ƙulla hulɗa da ƙungiyar BRICS bayan Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda da Uzbekistan.

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS

Gwamnatin Brazil ta sanar da cewa Nijeriya a hukumance ta shiga cikin jerin abokan hulɗar ƙungiyar ƙasashen duniya da tattalin arzikinsu ke bunƙasa da ake yi wa laƙabi da BRICS.

Brazil, wadda ita ce ke shugabantar ƙungiyar a 2025, ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a.

Nijeriya ta kasance ƙasa ta tara da ta ƙulla hulɗa da ƙungiyar BRICS bayan Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda da Uzbekistan kamar yadda Gwamnatin Brazil ta wallafa a shafinta.

Sanarwar ta bayyana cewa Nijeriya “ta ƙasance ƙasa da ke ƙara ƙarfafa hulɗar dangantaka tsakanin ƙasashen ɓarin kudancin duniya da kuma sauya salon shugabanci, wanda abu ne da Brazil ke bai wa muhimmanci.

“A matsayinta ta ƙasa ta shida mafi yawan al’umma a duniya, kuma mafi yawan al’umma a Afirka, kuma ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka, Nijeriya tana tarayya da manufofin ƙasashen ƙungiyar,” kamar yadda sanarwar ta ma’aikatar harkokin waje ta Brazil ta sanar.

BRICS, ƙungiya ce ta ƙasashe 10 da suka haɗa da Brazil, Rasha, Indiya, China, Afirka ta kudu, Masar, Habasha, Indonesia, Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Ana wa ƙungiyar kallon kini ta ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi ta duniya, wato G7.

A yayin taronta na 16 da ta gudanar a Kazan a watan Oktoban bara ne BRICS ta ɓullo da wannan sabon tsarin na bai wa ƙasashe damar ƙulla hulɗa da ita domin cimma muradunta.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS