Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya

Wannan zai zama wasa na farko tsakanin ƙasashen tun bayan shekarar 2005, lokacin da Nijeriya ta doke Gabon da ci 2-0.

Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya

A yammacin wannan Alhamis ce tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles za ta fafata da ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Wasan da za a buga da ƙarfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat, Morocco, zai zama wasa na farko tsakanin ƙasashen tun bayan shekarar 2005, lokacin da Nijeriya ta doke Gabon da ci 2-0.

Wannan wasan dai shi ne zai tabbatar da nasarar Nijeriya na samun tikitin shiga gasar kafin haɗuwar ta da Kamaru ko Dimokuraɗiyyar Congo a ranar Lahadi.

Wasan na zuwa ne ƙasa da awanni 24 bayan tawagar Super Eagles da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) sun warware matsalolin da suka shafi kuɗaɗe tsakanin ‘yan wasa da hukumomin ƙwallon ƙafa.

Kyaftin William Troost-Ekong ya tabbatar da cewa an biya dukkan haƙƙoƙin da suke bi, inda ya ce tawagar ta koma fili cikin karsashi da ƙwarin gwiwar neman nasara a wasan yau.

’Yan wasan Super Eagles sun nuna himma a atisaye — NFF

Ibrahim Musa Gusau, shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya (NFF), ya jaddada ƙwazon ’yan wasan Super Eagles wajen doke Gabon a wasan.

Gusau, wanda ke tare da tawagar a birnin Rabat, Morocco, ya ce ’yan wasan sun nuna ƙwazo a lokacin atisaye da kuma kishin ganin cewa Nijeriya ta samu tikitin buga gasar da Canada, Mexico da Amurka za su karɓi baƙunci a shekarar 2026.

Tun sama da shekaru 60 da suka wuce, Nijeriya ta samu nasara a wasa biyar daga cikin haɗuwa tara da Gabon. Sun yi wasa biyu a Libreville, inda Najeriya ta samu nasara ɗaya da canjaras ɗaya.

Nasara ɗaya tilo da Gabon ta taba samu ita ce a wasan neman gurbin shiga Kofin Duniya a ranar 25 ga Yuni 1989, inda ta doke Nijeriya 2-1, abin da ya hana Super Eagles zuwa gasar da aka yi a Italiya 1990.

Haka kuma, an tashi canjaras a wasa uku daga cikin haɗuwa tara, ciki har da na neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya da aka buga a Jamus a 2006.

Sai dai wannan fafatawar ta yau ba za ta yiwu a samu canjaras ba, domin dole ne a samu tawaga ɗaya tilo da za ta tsallaka zuwa karawar ƙarshe da za a yi ranar Lahadi, tsakanin wacce ta samu nasara da ƙasar Kamaru ko Dimokuraɗiyyar Congo.