Ninkaya a Kogin Fasahar Malam Sa’adu Zungur (10)
Wannan shi ne karo na goma kuma na karshe da GIZAGO (08065576011) ke ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ta hanyar bitar shahararren wakensa na ‘Arewa: Jumhuriya Ko Mulukiya?’ Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya: […]
Wannan shi ne karo na goma kuma na karshe da GIZAGO (08065576011) ke ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ta hanyar bitar shahararren wakensa na ‘Arewa: Jumhuriya Ko Mulukiya?’ Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya:
Masha Allahu, tafiya ta kammala hawa kuma ta zo gangara, har tana haramar taka birki. A wannan mako, za mu nazarci baitoci 27 na karshe a wannan mashahurin wake na marigayi Malam Sa’adu Zungur (Allah Ya jikansa da rahama)! Kafin sharhin, mu natsu tsam da tunaninmu, mu nazarci baitocin nan:
Tutocin Shaihu Mujaddadi,
Dada ba su zama Jamhuriya!
Insha Allahu! Mu tsarkake,
Bisa fatan za mu bi gaskiya.
Domin fa Arewa da hargitsi,
Da yawan barna, ba kariya.
Matukar a Arewa da karuwai,
Wallah za mu yi kunyar duniya.
Matukar ’yan iska na gari,
Dandaudu da shi da magajiya.
Da samari masu ruwan kudi,
Ga maroka can a gidan giya.
Babu shakka ’yan Kudu za su hau,
Dokin mulkin Najeriya.
Su yi kau sukuwa bisa kanmu, ko,
Mun roki zumuntar duniya.
Matukar yaranmu suna bara,
“Allah ba ku, mu sami abin miya!”
A gidan birni da na kauyuka,
Da cikin makarantun tsangaya.
Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu shakka sai mun sha wuya.
Matukar da musakai barkatai,
Da makaho ko da makauniya.
Ba muhalli nasu a Hausa duk,
Babu mai tanyonsu da dukiya.
Birni kauye da garuruwa,
Duk suna yawo a Najeriya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya,
Za ya sha kunya nan duniya!
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai nishadi, sai sharholiya.
Sai alfahari da yawan kwafe,
Girman kai, sai kwambon tsiya.
Camfe-camfe da tsibbace-tsibbacen,
Malaman karya, ’yan duniya.
Cin amana kuma da yawan riya,
Ga hula mai annakiya.
Babu mai aiki bisa hankali,
Da basira, don ya ga gaskiya.
Rantse-rantse da Allah yai yawa,
Ga karya, ga zambar tsiya.
Girman asali da na dukiya,
Sai ka ce dan “Annabi Fariya.”
Sai kinibibi, sai kwarmato,
Ga gulma da son kullalliya.
Wagga al’umma me za ta wo,
A cikin zarafofin duniya?
To, sarakai, sai fa ku himmatu,
Don ku gyara kasarku da gaskiya.
Kuma Allah Shi ne zai cika,
Ya kiyaye Arewa gaba daya!
Mun gode Allah Shi daya,
Don Shi ne Sarkin Gaskiya!
A yau da muke tsokacin nan, shekarar waken nan 66. Malam ya yi mana gargadi, ya yi mana hannunka-mai-sanda, ya yi mana bulala a wasu wuraren, duk domin mu kauce wa yaudarar ’yan duniya. Ya yi mana fatar cewa: “Tutocin Shaihu Mujaddadi, Dada ba su zama Jamhuriya. Insha Allahu! Mu tsarkake, Bisa fatar za mu bi gaskiya!” Sai dai kash! Malam, ba mu ji gargadinka ba, mun yi kunnen kashi, ba mu tsarkake zukatanmu ba, mun ki bin gaskiya; tuni muka shige Jamhuriya. Ai kuwa ga shi nan muna girbar bakar wahala da tozarci.
Malam da yake cewa: “Domin fa Arewa da hargitsi, Da yawan barna, ba kariya. Matukar Arewa da karuwai, Wallah za mu yi kunyar duniya.” Sai ga shi al’amarin a yanzu ya ta’azzara, ga hargitse-hargitse nan iri-iri – ga Boko Haram, ga rikice-rikicen addini, ga na kabilanci, ga fadan makiyaya da manoma, ga garkuwa da mutane don kudin fansa, abin ba a cewa komai. Maganar karuwai kuwa, abin ya zama ruwan dare. Karuwanci har lasisi gare shi a makarantunmu na zamani da wuraren ayyuka. Kunyar duniya kam an gama gamuwa da ita, sai dai fatar Allah Ya sa mu fadaka mu canja halayenmu, mu tuba.
Mu duba wadannan baitocin: “Matukar ’yan iska na gari, Dandaudu da shi da magajiya. Da samari masu ruwan kudi, Ga maroka can a gidan giya. Babu shakka ’yan Kudu za su hau, Dokin mulkin Najeriya.” Malam, Allah Ya kara maka ni’ima a makwancinka, amma dai lallai ’yan iska sun cika gari fal, daudanci da karuwanci sun kara samun wurin zama a cikin al’ummarmu. Wani abin takaicin ma, yanzu har kungiyoyi gare su, suna auren jinsi. Masu ruwan kudi kuwa, su ma sun cika ko’ina inda ake bushasha. Da dama fita suke zuwa kasashen ketare da sunan shakatawa. A yanzu kuwa makada da mawaka su ke da tagomashi a cikin al’ummarmu.
A wasu baitocin, Malam Zungur ya ce: “Matukar yaranmu suna bara, ‘Allah ba ku, mu sami abin miya!’ A gidan birni da na kauyuka, Da cikin makarantun tsangaya. Sun yafu da fatar bunsuru, Babu shakka sai mun sha wuya.” Ai kuwa abin da yake tabbata ke nan, duk birnin da ka duba a Najeriya da zarar ka ga yaro da kwanon bara, cikin tsummokara, kada ka raba daya-biyu, dan Bahaushe/Fulani ne, dan Arewa. Shan wuya kuwa yanzu muka fara , domin kuwa ba a dauki hanyar kawo gyara ba. Kato zai yi ta aure-aure, ya haifi yara, kawai sai ya kwararo su birni da sunan karatun addini. Bai san cinsu da shansu ba, bai san sutura ko maganinsu ba, balle wurin kwanciya.
A nan Malam Zungur ya yi gaskiya da ya ce: “Matukar da musakai barkatai, Da makaho ko da makauniya. Ba muhalli nasu a Hausa duk, Babu mai tanyonsu da dukiya. Birni kauye da garuruwa, Duk suna yawo a Najeriya.”
Malam tun yana da rai, Allah Ya haska masa ya gano abin da zai samu Malam Bahaushe, idan bai bi gaskiya ba. Malam Zungur ya ce: “Kai Bahaushe ba shi da zuciya, Za ya sha kunya nan duniya!” Saboda me kunya za ta cim masa? Malam ya ba da amsar cewa saboda: “A Arewa zumunta ta mutu, Sai nishadi, sai sharholiya. Sai alfahari da yawan kwafe, Girman kai, sai kwambon tsiya. Camfe-camfe da tsibbace-tsibbacen, Malaman karya, ‘yan duniya. Cin amana kuma da yawan riya, Ga hula mai annakiya. Babu mai aiki bisa hankali, Da basira, don ya ga gaskiya. Rantse-rantse da Allah yai yawa, Ga karya, ga zambar tsiya. Girman asali da na dukiya, Sai ka ce dan “Annabi Fariya.” Sai kinibibi, sai kwarmato, Ga gulma da son kullalliya.”
Daga karshe dai Malam Zungur ya kawo mana shawara, yadda za mu fita daga wannan kangi. Ya ce: “Wagga al’umma me za ta wo, A cikin zarafofin duniya? To, sarakai, sai fa ku himmatu, Don ku gyara kasarku da gaskiya. Kuma Allah Shi ne zai cika, Ya kiyaye Arewa gaba daya!” Ke nan matukar muka ci gaba da zama cikin sharholiya, muka ci gaba da abauce wa kyawawan nasihohin Malam Zungur, to babu wani abin kirki da za mu iya tsinanawa a zarafofin duniya.
Don haka, lallai ne mu tashi tsaye, shugabanninmu, malamanmu, sarakunanmu, talakawa, kowa da kowa mu dauki turbar gyara, mu tsaya kan gaskiya da aikin gaskiya. Sannan mu kama Allah, mu saki Shedan da hanyoyinsa. Kamar yadda Malam Zungur ya ce a baitinsa na karshe: “Mun gode Allah Shi daya, Don Shi ne Sarkin Gaskiya!”
Mun kammala!