Ninkaya a Kogin Fasahar Malam Sa’adu Zungur (5)
Wannan shi ne mako na biyar da GIZAGO (08065576011) ke ci gaba da ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ma ta hanyar bitar shahararren wakensa na “Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya? Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki […]
Wannan shi ne mako na biyar da GIZAGO (08065576011) ke ci gaba da ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ma ta hanyar bitar shahararren wakensa na “Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya? Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya. Ga kashi na biyar:
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu! Gaisuwa gare ku tare da darajawa ga malamaina, ’yan uwa da abokan arziki da ke bibiyar wannan shafi. Kamar yadda muka faro, a yau ma za mu ci gaba da ninkaya, karo na biyar, a kandamin Kogin Hikima da Fasahar marigayi Malam Sa’adu Zungur. A wannan karo, za mu yi tsokaci, nazari da tambihi bisa baitoci 15 da ke kasa, wadanda na tsakuro daga mashahurin wakensa na ‘Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya?’
Ya Ja’afaru, zo ka wuce gaba,
Malami ne, Sarkin duniya.
Mallawa, su da Barebari,
Sun ga adalcinka da gaskiya.
Katsinawa, har da Zagezagi,
Sullubawan Lardin Zariya.
Duka sun san kai ne shugaba,
Ka rike zarafinsu da gaskiya.
Za mu bi ka, ka ja mu zuwa gaba,
Kar ka yarda Arewa ta sha wuya!
A kasar Adamawa da Ahmadu,
Lamido fitillun gaskiya.
Mun kai masa caffa har gida,
Allah sudda asiri a duniya!
Jikan Modibbo Subado, sai
Ka tsare daularka da gaskiya.
Jaumirawo ya taimaki Julbe duk,
Don su san girma a Najeriya.
Madalla, Muhammadu mai Muri,
Sarkin da ya hangi dari daya.
Ko Lugard ya san himma tasa,
Da irin kwazonsa a duniya.
Kyakkyawar fata kewano,
Inji Kenci, a yamma da Zariya.
Hakki na Nufawa na wuyan
Ndayako, Etsu abin biya.
Ga Umaru Sanda a Guddiri,
Malami ne ya san gaskiya.
A Misau ga Sarki Ahmadu,
Malami ne tun a mazan jiya.
A wadannan baitoci, Malam ya ci gaba da fadakarwa dangane da abin da ya shafi al’amura da rayuwar al’ummar Arewa. A lokacin da Malam Zungur ya kattaba wannan wake, shekara 66 da suka gabata, ya yi la’akari da matsalolin rayuwa da suke addabar al’ummar Arewa, matsalolin da yake ganin cewa idan suka ci gaba, za su kassara ’ya’ya da jikokin-jikokin al’ummar wannan yanki har illa masha Allahu. Don haka Malam Zungur ya ankara cewa ana son yi wa al’ummar Arewa balulluba da tsarin Jamhuriya, wanda zai kwace mulki daga hannun shugabanni na kwarai, zuwa ga ashararai. Wannan ke nuna cewa mulki, al’amari ne mai matukar muhimmanci da ke taka rawa ga ci gaba ko lalacewar al’umma.
A wadannan baitoci 15 na sama, Malam Zungur ya bayyana mana siffofi da ginshikan mulki na kwarai, kamar kuma yadda ya bayyana mana siffofin wanda ya cancanci ya zama mai mulki. Yaya abin yake?
Siffofin shugaba na kwarai sun hada da ilimi, adalci, gaskiya da himma.
Domin mu gane abin dalla-dalla, Malam Zungur ya doka mana misali da adalan shugabannin al’umma na zamaninsa da kuma magabatansu. Ya ambaci sunan Sarkin Zazzau Malam Ja’afaru, wanda ya bayyana da mutum Malami (mai ilimi), Adali, wanda ke gudanar da mulkinsa cikin adalci ga al’ummarsa. Sannan ya kasance mai Gaskiya, wanda gaskiyarsa ta bayyana ga al’ummarsa da yake mulki, wadanda suka kasance Zagezagi, Mallawa, Barebari, Katsinawa da sauransu.
Haka kuma Malam Zungur ya kama sunan Lamidon Adamawa, Ahmadu, wanda ya bayyana da “Fitillun Gaskiya.” Ke nan shi mai gaskiya ne kuma tambari na gaskiya, wanda ke koyar da al’umarsa su yi gaskiya.
Malam Zungur bai gushe ba, ya ambata sunan Sarkin Muri Muhammadu, wanda ya ce mutum ne shi mai himma da kwazo, mai yin hidima ga al’ummarsa. Ya bayyana cewa hatta Baturen Mulki, Lord Lugard ya shaida irin kwazonsa. Wannan jan hankali ne ga duk mai son zama mai mulki nagartacce, to ya kasance mai kwazo da himma, mai ilimi, mai gaskiya da adalci, kamar wadannan sarakuna da Malam Zungur ya ambata.
Malam bai tsaya nan ba, sai da ya ambata Etsu Nupe, Ndayako da Sarkin Guddiri (a Jihar Bauchi), Umaru Sanda da kuma Sarkin Misau Ahmadu. Malam ya ja hankalinsu da su ci gaba da mulkinsu na adalci kuma su tsaya kai da fata, kada su bari Arewa (al’ummarsu) su fada cikin wuya. Ma’ana, kada su bari a raba mutane da tsarin mulkin gaskiya na Mulukiya.
Ya ku ’yan uwa, a wannan gabar, mu tsaya tsam da ranmu mu yi tunani. Shin a yau yaya al’amura suka kasance? Shin an raba mu da tsarin mulkin adalci, an maye mana shi da gurbatacce ko kuwa? Shin abin da Malam Zungur ya tsoraci ya faru da mu, yana faruwa ko kuwa? Shin yaya tsarin mulkinmu da masu mulkinmu suka kasance a yau? Shin ana gudanar da mulki da Ilimi, Gaskiya, Adalci da Himma domin jin dadin al’umma ko kuwa? Ruwa a cokali, inji masu iya magana, ya ishi mai hankali wanka.