Ninkaya a Kogin Fasahar Malam Sa’adu Zungur (7)
Wannan shi ne karo na bakwai da GIZAGO (08065576011) ke ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ta hanyar bitar shahararren wakensa na ‘Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya? Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya: A yau kuma […]
Wannan shi ne karo na bakwai da GIZAGO (08065576011) ke ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ta hanyar bitar shahararren wakensa na ‘Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya? Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya:
A yau kuma da ikon Allah, mun tsamo baituka 13 ne daga wannan mashahurin wake na ‘Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya,’ kuma za mu bi su mu kwankashe su domin fitar da ma’anoni da nasihohin da za su ankarar da mu, da nufin saita zamaninmu, domin mu dace, insha Allahu.
In sunka sake jama’ar Kudu,
Suka hau mulkin Najeriya.
Dada ba sauran mai tambaya,
Kowa ya san zai sha wuya!
An sha bamban bisa kan nufi,
Na shirin mulkin Najeriya.
Niyyar Kudu in suka daukaka,
Duk kasa ta zamo Jamhuriya.
Mu kam niyyarmu a karkasa,
Don Arewa ta zabi Mulukiya.
Ku fahimci shiri na Mulukiya,
Da yawan hadarin Jamhuriya.
Sarki da gidajen shawara,
Da shari’a, kun ji Mulukiya.
Mulki na wakilai gurguzu,
Ba Sarki babu Sarauniya.
Sai ’Yan sanda, sai Soja, sai,
Oda, ita ce Jamhuriya.
Fatarmu Arewa ta farga duk,
Don ta gane lamirin duniya.
Farfagandar makirci duka,
Sai a bar ta, a binciki gaskiya.
Hudubobin kinibibi duka,
Dangin zance na filaniya.
A jaridu ko a matattara,
A wurin lacca da hatsaniya.
Malam Zungur bai gushe ba, yana ja kunnuwanmu mutanen Arewa, cewa ahir dinmu da amincewa da bara-gurbin tsarin mulki mai taken “Jamhuriya” saboda kamar yadda ya ce: “In sunka sake jama’ar Kudu, Suka hau mulkin Najeriya. Dada ba sauran mai tambaya, Kowa ya san zai sha wuya!” Shin ta yaya za mu yi saurin fahimtar wannan gargadi da ke cikin baitocin nan biyu?
Mu duba baitoci na gaba, wadanda ke cewa: “An sha bamban bisa kan nufi, Na shirin mulkin Najeriya. Niyyar Kudu in suka daukaka, Duk kasa ta zamo Jamhuriya.” Wannan ke nuna cewa akwai bambance-bambance a tsakanin yankunan Arewa da Kudu dangane da abin da ya shafi Manufa, Addini, Al’ada da Akida. Don haka abu ne mai tsananin wahala a samu daidaito da fahimta da aminci a tsakanin al’ummun da suka sha bamban ta wadannan fuskoki.
Kafin dunkulewar Najeriya zuwa kasa daya a 1914, inda aka hada yankin Arewa da yankin Kudu, idan muka dauki wadannan tubala hudu da muka ambata a shadarar da ta gabata, za mu kara fahimtar dalilin da ya sa Malam Zungur ya ambaci cewa lallai mu kiyayi mutanen Kudu.
Bari mu dauki Addini da farko: Tun kafin zuwan Turawa yankin da a yau ake kira da Najeriya, Yankin Arewa na da tsarin addinin Musulunci, wanda ya shahara, ya samu fadada. Daular Musulunci, musamman bayan Jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo a 1804 ta kafu kuma ta karfafa. Tsarin mulki da tsarin rayuwa, duk na Musulunci ne. Alhali yankin Kudu ba su da wani tsayayyen addini mai girma daga Allah, sai na gargajiya wanda ya dogara da bautar gumaka da tsatsube-tsatsube. Bayan zuwan Turawa ne suka samu nasarar dasa addinin Kirista a yankin.
Don haka, a yayin da Arewa ke da karfin addinin Musulunci, yankin Kudu shi kuma, musamman bayan zuwan Turawa, yana da karfin addinin Kirista. Wannan bambanci na addini, babu shakka ya fara taka rawar kawo rashin daidaito da rashin fahimta a tsakanin al’ummar yankunan biyu tun daga lokacin da aka samar da kasa daya a 1914 har zuwa yau da muke sharhin nan.
Manufa: Haka ma idan muka duba, kamar yadda Zungur ya fada, akwai bambancin nufi tsakanin al’ummar Arewa da ta Kudu. Babbar manufar mutanen Kudu ita ce har kullum DUNIYA. Babu ruwansu da wani tunanin adalci, gaskiya da kyautatawa a tsakanin mutane, su dai su samu duniya da abin cikinta, ko ta yaya ta zo. A hannu daya kuma, manufar al’ummar Arewa tana da wani abu da ke yi mata saiti, tana da addini, wanda ke mata jagora. Bayan duniya, suna tunanin akwai wata rayuwa ta gobe, wato Lahira. Don haka addini na taka rawa wajen rayuwarsu ta cewa a yi adalci, a yi gaskiya wajen gudanar da rayuwa.
Al’ada: Ta fuskar al’ada ma, akwai bambanci mai girma tsakanin al’ummar Arewa da Kudu. A Arewa, tun bayan Jihadin Shehu Dan Fodiyo, sakamakon mamayewar Musulunci ga manyan kabilun Hausawa da Fulani da Barebare, al’ada ta zama kusan abu daya da Musulunci ta fuskoki da dama, wadanda suka hada da dabi’a, sutura, zamantakewa, aure, aiki ko sana’a ko kasuwanci da mulki da shari’a. A Kudu kuwa, duk da cewa suna da kabilu daban-daban masu yawa, amma su ma al’adunsu na rayuwa sun garwaye da na Turawa ko kuma mu ce da Kiristanci. Don haka akwai bambancin yadda al’ummomin biyu ke kallon rayuwa.
Akida: Ta fuskar akida ma, an sha bamban tsakanin al’ummun Arewa da na Kudu. Tarbiyya da tsarin rayuwar mutane ba iri daya ba ne.
Ta yaya za mu kara tabbatar da ma’anar kalaman Malam Zungur, na cewa idan mutanen Kudu suka hau mulkin Najeriya, kowa zai sha wuya? Sai mu waiwayi tarihi. Wa ya kitsa kuma ya aiwatar da juyin mulkin 1966? Mutanen Kudu, musamman Kudu-maso-Gabas ne suka yi uwa da makarbiya wajen haddasa aika-aikar da ta zama dan ba ga tagayyara al’ummar Arewa a fuska daya da ma Najeriya baki daya a daya fuskar. A wannan lokaci ne Arewa/Najeriya ta yi rashin muzakkaran shugabanni masu adalci da kishin kasa, shugabannin da suka sadaukar da rayuwarsu domin ci gaban al’umma. Kadan daga cikinsu akwai Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da sauransu.
Mu duba kuma tun daga lokacin har zuwa yau, yadda al’amuran mulki da tafiyar da tattalin arzikin kasa da aikin gwamnati da sauransu, kusan duk mutan Kudu sun mamaye. Ka tsaya tsaf ka natsu, ka duba kasuwanninmu da dukkan sha’anonin rayuwa, za ka ga mutanen Kudu sun mamaye.
Kamar yadda Malam Zungur ya bayyana, tsarin mulkin Mulukiya, shi ya fi dacewa da Najeriya, muddin dai Arewa na so ta dore da tsarinta na baya, domin kuwa Sarki da gidajen shawara da shari’a su ne tsarin Mulukiya, wanda ya sha bamban da Jamhuriyya, wanda ya ta’allaka da mulkin wakilai gurguzunsu. Sarki ko Sarauniya ba su da ta cewa. Za a mayar da su sai rawani amma ba karfin mulki. Ga shi kuwa ta tabbata, tunda a tsarin da Najeriya take kai yanzu, Shugaban Karamar Hukuma na gaba da Sarki mai daraja ta daya a yankinsa, ta fannin mulkin al’umma.
A tsarin Jamhuriya, babu abin da ke tasiri illa farfaganda da makirci, ba gaskiya da adalci ba. Haka kuma sai hudubobin kinibibi da gutsuri-tsoma a jaridu da mujallu. Yanzu kuma ga shi abin ya tumbatsa har a Soshalmidiya. Sai kuma hatsaniya da haddasa rikice-rikicen addini da kabilanci da bangaranci don kishin yanki ko don biyan bukatun wadansu tsiraru. Idan mun yi nazarin Najeriya a mulkin siyasar zamani, za mu ga cewa wannan zance na Malam Zungur shi ya tabbata.