Ninkaya a Kogin Fasahar Malam Sa’adu Zungur (8)
Wannan shi ne karo na takwas da GIZAGO (08065576011) ke ci gaba da ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ma ta hanyar bitar shahararren wakensa na ‘Arewa: Jumhuriya Ko Mulukiya?’ Waken na cike da darussan da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa […]
Wannan shi ne karo na takwas da GIZAGO (08065576011) ke ci gaba da ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ma ta hanyar bitar shahararren wakensa na ‘Arewa: Jumhuriya Ko Mulukiya?’ Waken na cike da darussan da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya:
A wannan karo da ikon Allah za mu nazarci baitoci 15 ne na wannan mashahurin wake. Bari mu zayyano su tukunna daga bisani mu bijiro da sharhi tare da tsokaci:
Allah Ya kiyaye Najeriya,
Ga masifar Lardin Indiya.
“Tsoron Allah am magani,”
Shi dai ka kiyaye Mulukiya.
Mu dai hakkinmu gaya muku,
Ko ku karba ko ku yi dariya.
Dariyarku ta zam kuka gaba,
Da ladamar mai kin gaskiya.
Wa’azi ne mulkin Indiya,
Da ta zam Daular Jumhuriya.
Yau ina manya na sarakunan,
Pakistan ko kuma Indiya?
Da Nizam, Maharaja da Raja duk,
Sai kuka ba mai dariya.
Da sarakai sun fi dari biyar,
Duka sun watse ba ko daya.
Sai ka ce fa dadai ba a yi su ba,
Kun ji sharrorin Jumhuriya.
A mujallar “Daily Mail” akwai,
Tarihin mulkin Indiya.
Da abin da ya faru a bara duk,
Bisa rushe gini na Mulukiya.
Ko a Burma akwai sauran iri,
Na sarakai? Sai ku yi tambaya.
Indonesiya su ma sun rage?
Kaito, tsarin Jumhuriya!
Duk misalan nan na Amurka ba,
Mai kyau na shirin Jumhuriya.
Kar ku rudu da zancen ja’irai,
Masu son halakar Najeriya.
Malam Zungur yana ci gaba da yi mana gargadi, domin mu fahimci illar tsarin Jumhuriyya. Ya yi amfani da tarihi, ya nemi mu dauki darasi. Ya ce: “Allah Ya kiyaye Najeriya, Ga masifar Lardin Indiya.” Ke nan kasar Indiya ta taba samun kanta a balahirar tsarin Jumhuriyya kuma ba ta ji da dadi ba.
Amma daga yadda duniya ta rika canjawa, Yahudu da Nasara suka taso al’ummar duniya da wannan tsari, babu yadda za a guje wa sharrin Jumhuriyya sai ta hanyar tsoron Allah da bin dokikinSa. Musamman ga masu mulki, sai sun sanya gaskiya da adalci a lamurran mulki. Su kuma al’umma sai sun bi tafarkin Allah, kafin su samu sa’ida. Kamar yadda Malam ya yi nasiha, a wannan baitin: “Tsoron Allah am magani,” Shi dai ka kiyaye Mulukiya.”
Kuma an samu bayanai dalla-dalla hatta daga Alkur’ani da hadisan Manzon Allah (SAW), cewa tsoron Allah na tabbatar da rayuwa mai sauki kuma mai fa’ida ga al’umma. A yayin da kuma zalunci da sabon Allah kan jefa al’umma cikin ukuba da masifa.
An samu wani Hadisi daga Abu Zarri Jundub bin Junadah da Abu Abdurrahman Mu’az bin Jabal (Allah Ya yarda da su), cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ka zama mai tsoron Allah a duk inda kake kuma ka bi mummunan aiki da kyakkyawan aiki da zai goge mummunan. Kuma ka yi kyakkyawar mu’amala da mutane.”
Wannan ke kara tabbatar mana da abin da Malam Zungur ya bayyana cewa tsoron Allah ne kadai zai mana maganin duk wata barazana. Kamar yadda Hadisin nan ya nuna kuma, koda mun aikata wani mummunan aiki bisa kuskure ko saboda ajizancinmu na ’yan Adam, to mu yi kokarin aikata wani kyakkyawan aiki da zai goge mummunan. Kuma Hadisin ya neme mu rika gudanar da kyakkyawar mu’amala a tsakaninmu da mutane. Ma’ana, kada mu cutar kuma kada a cuce mu.
Haka kuma, akwai bayanin da ke jan hankalin masu mulki da su rika mulkin jama’a da gaskiya da adalci, bayanin da ke cewa: “Mulkin adalci na dorewa koda a hannun kafiri ne kuma mulkin zalunci yana rugujewa koda a hannun Musulmi ne.”
Wani karin bayanin kuma shi ne, lallai tsoron Allah da guje wa aikata alfasha su ne hanyoyin tabbatar da ci gaban al’umma. Misali, an samu wani Hadisi da ke cewa, munanan ayyuka biyar, matukar al’umma na aikata su, to za su haifar da munanan sakamako biyar ga wannan al’umma.
Na daya, idan aikata zina ya yawaita a kasa, Allah zai jarabci al’umma da cututtuka marasa jin magani da mace-mace. Na biyu, idan cin riba ya yawaita a kasa, Allah zai jarabci al’umma da talauci. Na uku, idan mutane suka hana zakka, Allah zai hana al’umma ruwan sama. Na hudu, idan al’umma suka rika tauye mudu, suka bayyanar da ha’inci a kasuwanci da sauran sha’anoninsu, to Allah zai jarabci kasa da fari. Na biyar kuma, idan al’umma ta daina aiki da Alkur’ani, Allah zai jarrabi mutane da rarrabuwar kai da rashin fahimtar juna.
Don haka, Malam Zungur ya yi gaskiya da ya gargade mu da mu kasance masu tsoron Allah, wanda shi ne kadai maganin duk wata musifa.
A baitoci na gaba, Malam ya ce: “Mu dai hakkinmu gaya muku, Ko ku karba ko ku yi dariya. Dariyarku ta zam kuka gaba, Da ladamar mai kin gaskiya.” Hakan ke nuna cewa a matsayinsa na mai fadakarwa, ya fita hakkin al’umma, ya yi nasiha, ya fayyace gaskiya. Ya rage ruwan shugabannin da al’umma su yi amfani da wannan nasiha ko su jefar. Idan suka jefar, to kuwa karshenta su yi nadama.
Abin tambaya a nan shi ne, shin al’umma da shugabannin Arewa sun yi amfani da nasihar Malam Zungur kuwa? Ni dai a bincikena, ba a yi ba. Shi ya sa ma a yanzu muke cikin nadama. Idan muka lura tsaf, al’ummarmu na cikin matsaloli daban-daban. Muna aikata abin da muka ga dama, ba mu tsoron Allah. Ga talauci, ga jahilci, ga kaskanci duk sun baibaye ko’ina a Arewa. Don haka ya kamata mu taru mu yi karatun-ta-natsu, mu dauki shawarar Malam Zungur, domin mu fita daga wannan matsala.
A baitoci na gaba, Malam Zungur ya kara bayyana mana yadda sharrin Jumhuriya ya daidaita Indiya, wacce ta zauna shekara 190 a mulkin mallakar Turawan Birtaniya, har sai a 1947 ta samu mulkin kai. Ya kuma nuna mana yadda ta faru da kasar Burma, wacce ita kuma ta samu ’yancin kai a 1948, wadda ta kasance cikin mulkin mallakar Turawan Birtaniya tun daga shekarar 1824. Ya kuma doka mana misali da kasar Indonesiya, wacce ita kuma sai a 1945 ta samu ’yanci daga mulkin Turawan Holland.
Malam Zungur ya yi mana gargadi da mu kiyayi zuga da kinibibin Amurka, inda a wadannan baitoci biyu ya ce: “Duk misalan nan na Amurka ba, Mai kyau na shirin Jumhuriya. Kar ku rudu da zancen ja’irai, Masu son halakar Najeriya.”
Sai dai kash! Ba mu ji wannan gargadi ba, sai da ta kai ga an zuga mu muka fafata Yakin Basasa na tsawon shekara uku (1967-1970) kuma tun daga lokacin nan har zuwa yau, babu cikakkar jituwa tsakanin al’ummominmu na Arewa da na Kudu. Ba ma wancan lokacin ba, hatta a wannan zamanin muna fuskantar ingiza mai kantu ruwa daga wasu manyan kasashen Turawa ’yan Jari-Hujja, suna haddasa rashin jituwa tsakanin al’ummominmu. Karamin misali shi ne yadda Kungiyar IPOB ta kabilar Ibo a karkashin Nnamdu Kanu ke yunkurin wargaza Najeriya.
Lallai ya kamata al’ummar Arewa ta waiwayi baya, ta dauki nasiha daga fasihin malami, marigayi Sa’adu Zungur, domin kauce wa da-na- sani, wacce masu iya magana suka ce keya ce.