Nishadantarwa ta sa Bapalasdinuwa zama wadda ta fi iya koyarwa a duniya
Hanan Al Hroub ce malama mafi nagartar koyarwa a duniya, wadda dabarun koyarwarta suka nuna tana gwama nishadi da karantarwa, don haka aka zabeta bana. daliban malama Hanan da ke makarantar sakandare ba sa kaunar rashin halartar darussanta ba. Domin takan yi ado da tufafi launin ja mai daukar ido, inda takan rike butunbutumin biri, […]
Hanan Al Hroub ce malama mafi nagartar koyarwa a duniya, wadda dabarun koyarwarta suka nuna tana gwama nishadi da karantarwa, don haka aka zabeta bana. daliban malama Hanan da ke makarantar sakandare ba sa kaunar rashin halartar darussanta ba. Domin takan yi ado da tufafi launin ja mai daukar ido, inda takan rike butunbutumin biri, al’amarin da ke jan hankalin daukacin daliban da ke cikin ajin.
A shekarar da ta wuce cibiyar barkey foundation ta dauki nauyin karrama malami ko malmar da ya/ta fi iya koyarwa a duniya, in data rika bayar da kyautar Dala miliyan guda don tallafa wa malaman a kasashen su. A bana dai Hanan al Haroubi malama a kasar Palasdinu ce ta ci wannan kyauta
“daukacin darussan ajina ana fara su ne da waka,” a cewar Hanan, lokacin da take rera wakokin larabci ga ’yan ajin raino, don karfafa gwiwar yaran ajinta suka rika yin waka su kadai.
Ranar da ta gudanar da darasi na musamman, a ranar baje kolin dabarun koyarwa na duniya a shekarar 2016, ajin Hanan ya yi matukar kayatarwa, inda kowa ke jin dadin darusssa tare da bayar da gudunmuwa a tsakanin manya da kananan dalibai.
Wannan gwarzuwa da ta ci kyautar malama mafi nagartar koyarwa ta duniya a shekarar 2016, ta yi nuni da cewa, taken aikinta, shi ne, “ban yarda da tashin hankali ba,” sannan tana amfani da dabarun kwararru wajen kara samun kwarewa a aikinta, kamar yadda yake kunshe a littafinta mai taken “Mu yi wasa, mu koyi karatu.”
Wannan malama da ke koyarwa a makartantar Sakandare ta samiha Khalil da ke Al Bireh, a Palasdin: Hanan ta taba zama ’yar gudun hijira, wadda ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira da ke garin Bethlehem. A lokacin da take karama ta sha fama da tashe-tashen hankula. Ta shiga harkar koyarwa a firamare haikan bayan da ’ya’yanta suka shiga cikin rudani a sanadiyyar harbe-harben tashin hankali da suka gani a hanyar su ta zuwa gida bayan sun dawo daga makaranta.
Mafi yawan dalibaina sun fito ne daga sassan da ake fama da tashe-tashen hankula. Sun hadu da matsaloli na tashin hankali, sannan na taba ganin inda dalibai ke duka da cizon yaran aji, kusan sau hudu ko biyar a rana guda,” kamar yaedda Hanan ta bayyana wa Jaridar Khaleejtimes bayan da ta gabatar da darasin aji na musamman.
“A lokacin da na kawo dauki a harkar koyarwa rikice-rikice da fadan dalibai ya yi matukar raguwa cikin kwana biyu kacal, kai an ma daina samun tashe-tashen hankula (a makaranta) bayan wata guda,” inji ta.
Dabarun koyarwarta
Hanan kan fara darasin jinta da jefa balan-balam mai dauke da lamba da kan fada hannun dalibanta.
“Alal misali, idan balan-balan din na dauke da lamba tara (9), sai dalibai su ambaci lambobi biyu da idan aka tara su za su bayar da tara, sannan su jefa balan-balan din ga sauran dalibai,” inji ta.
Yara na son a nishadantar da su a lokacin da suke koyon karatu, inda ta kara da cewa, “irin wadannan dabarun kan dauke hankalin su daga matsalolin rayuwa da suke fuskanta, sannan su samu kwarin gwiwar tunkarar abin da suka sa a gaba.”
Dabarun koyarwar Hanan suna da sauki, ga kuma matukar tasiri. Takan raba dsalibanta gungu-gungu ko gida hudu zuwa biyar. Kowane gungu akanm ba shi aikin cajin kwakwalwa da ake son ya kammala cikin takaitaccen lokaci. “daukacin kayan aikin koyarwa da nike amfani da su, an taba amfani da su a gida, sai mu sake yin amfani da su,” a cewar Hanan, inda ta bayar da misali da daya daga cikin ajujuwan da take kula da su.
Hanan na amfani da dimbin kayan wasanni wajen koyar da darussan aji, al’amarin da ya mayar da karantarwarta tamakar gwama nishadi a cikin koyarwa.
“Ajujuwan mu sun cika fiye da ka’ida a Palasdinu, inda ake samun fiye da dalibai 35 a aji guda. Wasu daga cikin ajujuwan ba su da kayan inganta koyarwa,” inji ta.
An yi bukukuwan murna a birnin Ramallah bayan da aka sanar da nasarar Hanan Al Hroub a matsayin malamar da ta fi iya koyarwa a duniya, cikin shekarar nan ta 2016.