NLC na neman durƙusar da arziƙin Najeriya — Fadar Shugaban Ƙasa
NLC da TUC sun shiga yajin aiki kan rashin cimma yarjejeniya a kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
Gwamnatin Tarayya, ta mayar da martani game da yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago NLC da TUC, suka domin buƙatar ganin an mayar da mafi ƙarancin albashi Naira 494,000 don magance matsalar tsadar rayuwar da ta addabi al’ummar Najeriya.
Da yake bayani a wani gidan talabijin na Channels, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce buƙatar ta ‘yan ƙwadago ba za ta yi komai ba face kassara tattalin arzikin ƙasar nan.
- Chelsea ta naɗa Maresca a matsayin sabon kocinta
- NLC ta kashe wuta daga babbar cibiyar lantarkin Najeriya
Ngelale, ya ce matuƙar gwamnati za ta biyewa buƙatar ƙungiyoyin ƙwadagon, tabbas wasu daga cikin kamfanoni masu zaman kansu za su rufe, abin da zai zamarwa ƙasar nan matsala a maimakon samun ci gaba.
Ya ce ko a yanzu Najeriya na fama da tsadar kayan abinci da sauran kayan buƙata, kuma babu makawa wannan lamarin zai ƙaru matuƙar aka yi ƙarin albashin da ƙungiyar ƙwadago ke buƙata.
Kawo yanzu dai Gwamnatin Tarayya, ta amince da biyan Naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin, to sai dai NLC ta yi fatali da wannan buƙatar.
NLC ta fusata ne bayan ƙoƙarin tatatunawa da Gwamnatin Tarayya domin cimma yarjejeniya dangane da mafi ƙarancin albashin ya gagara, ganin yadda gwamnatin ta dage kan cewar Naira 60,000 kawai za ta iya biya.
A ranar Litinin NLC da TUC suka fara yajin aiki, lamarin da ya durƙusar da harkokin yau da kullum a faɗin Najeriya.