NLC na neman goga wa Tibubu bakin jini —Fadar Shugaban Kasa

Yajin aikin NLC da TUC ya tsayar da harkoki a sassan Najeriya

NLC na neman goga wa Tibubu bakin jini —Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Kasa ta soki yajin aikin da kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC suka shiga, tare da zargin kungiyoyin da kokarin ba ta wa Gwamnatin Tinubu suna.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya ya bayyana rashin jin dadinsa da yajin aikin, kasacewar akwai umarnin kotun masana’antu ta kasa da ta hana NLC da TUC tafiya yajin aikin.

Aminiya ta ruwaito cewa yajin aikin ya tsayar da harkoki a sassan Najeriya, a sakamakon biyayya ga umarnin uwar kungiyar kwadaga na fara yajin aikin da kungiyoyin malamai, da na ma’aikatan lafiya, da na sufuri da na wutar lantarki da na ma’aikatan majalisun dokoki da sauransu suka yi.

A cewar Bayo Onanuga yajin aikin wanda ya tsayar da harkoki a Najeriya “da NLC da TUC suka yi ba komai ba je face son rai da yunkurin goga wa gwamnati bakin jini,

“Har yanzu mun rasa dalilin da NLC da TUC suka yanke shawarar hukunta mutane sama da miliyan 200 a kan wani lamari da ya shafi shugaban NLC, Joe Ajaero,” in ji sanarwar.

Makonni biyu da suka wuce ne aka lakada wa Ajaero dukan tsiya a Jihar Imo.

NLC ta zargi ’yan sanda da gwamnatin Imo a lamarin, amma kowanne daga cikin wadanda ake zargin ya nesanta kansa.

Gwamna Hope Uzodinmna na Imo ya nesanta kansa da abin da aka yi wa Ajaero, duk da cewa ya zargi shugaban na NLC da tsoma baki a harkokin siyasar jihar.

A gefe guda kuma, ’yan sanda sun bayyana cewa sun kai Ajaero ofishinsu ne domin ba shi kariya daga masu neman kai masa hari.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake gab da zaben gwamnan jihar, wanda Uzodimna ke neman wa’adi na biyu — wanda yanzu ya lashe.

A kan haka ne Sufeto-Janar na ’yan sandan Najeriya ya sauya wa kwamishinan ’yan sandan Imo wurin aiki ya kuma ba da umarnin a gudanar da bincike.

Wannan takaddama ce ta sa kungiyoyin kwadagon bai wa Gwamnatin Tarayya kwanaki 10 ta yi abin da ya dace game da halin matsi da ake fuskanta a kasar nan.