NLC ta kira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun karin albashi
Gwamanti ta jingine batun karin albashi domin Shugaba Tinubu ya kara tuntubar masu ruwa da tsaki kafin mika lamarin ga Majalisar Dokoki ta Kasa.
Uwar Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta kira taron gaggawa bayan Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta jingine maganar karin mafi karancin albashi.
Kungiyoyin kwadagon za su yi zaman ne da misalin karfe 10 na safiyar Laraba a Abuja, bayan matakin da Gwamnatin Tarayya ta jingine wasikar da ta fitar da farko kan karin mafi karancin albashin domin ba wa Shugaba Tinubu damar fadada tuntubar bangarorin da lamarin ya shafa.
Sun sanar da haka ne bayan Ministan Yada Labari da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya sanar bayan taron Majalisar Zartaswa a ranar Talata cewa batun karin albashin ne kawai ba a tattauna a zaman da aka cimma matsaya kan abubuwa 39 da ke kunshe cikin ajandar taron ba.
Ministan ya bayyana cewa kafin zaman an karbi rahoton kwamitin karin albashin da ya kunshi matakan gwamnati uku da kungiyar kwadago da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
- An gabatar da ƙudurin gyara masarautar Sarkin Musulmi a Sakkwato
- DAGA LARABA: Shirin Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Magance Matsalar Tsaro
Sai dai, a cewarsa, Majalisar Zartaswa ta jingine aiwatar da umarnin karin mafi karancin albashin ne saboda al’amarin ya shafi duk bangarorin — gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi, kamfanoni masu zaman kansu da ’yan kwadago.
A cewarsa a yi hakan ne domin Shugaba Bola Tinubu ya kara tuntubar masu ruwa da tsaki kafin mika lamarin ga Majalisar Dokoki ta Kasa.
Bayan nan ne wani jigon a kungiyar NLC ya tabbatar wa Aminiya a daren Talata cewa shuagabancin kungiyoyin zai yi zaman gaggawa domin cimma matsaya kafin shugaban kasa ya tuntube su yi kan lamarin.
“Duk da cewa mun riga mun yanke shawara, amma za mu sake zama ranar Laraba da safe domin sake duba lamarin kafin su (gwamnati) tuntube mu.
“Zaman na da muhimmanci,” inji babban jami’in na kungiyar kwadago.
A farkon watan nan na Yuni ne kungiyoyin kwadago suka shiga yajin aikin kwana biyu da ya tsayar da harkoki cak a Najeriya.
Sun yi yajin aikin ne domin neman karin mafi karancin albashin da har yanzu ake ci gaba da kai ruwa rana tsakaninsu da bangaren gwamnati.