NLC ta nemi ’yan Najeriya su yi watsi da dokokin haraji
Shugaban NLC ya ce dole ne ‘yan Najeriya su haɗa kai wajen neman adalci kan abin da ya shafe su.
Shugaban NLC, Joe Ajaero
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), ta buƙaci ’yan Najeriya kada su amince da dokokin haraji da aka yi wa cushe.
Shugaban NLC, Joe Ajaero ne, ya bayyana a saƙonsa na Kirsimeti na 2025, inda ya ce an yi wa wasu dokokin harajin cush ko sauye-sauye.
- An kashe mutum 5 a sabon hari a Binuwai
- NAJERIYA A YAU: ‘Halin Kunci Da Muke Ciki A Sansanin Gudun Hijira Yayin Bikin Kirsimeti’
Ya ce, “Dole ne mu nemi adalci a kan haraji, inda masu kuɗi su biya nasu, kuma a cire duk wani haraji da ke ci wa talakawa.
“Duk wata doka ta haraji da aka sauya ko aka yi wa cushe, kada a amince da ita.”
Ajaero, ya ƙara da cewa, yana da kyau a tsara doka cikin tsari maimakon a gaggauta yin ta ɗauke da kurakurai.
Har ila yau, ya bukaci ’yan Najeriya su kasance masu haɗin kai wajen neman adalci a al’amuran da suka shafi mulki.
Tuni dai Majalisar Wakilai ta fara bincike kan wasu dokokin harajin da aka yi wa sauye-sauye.
Kwamitin da Muktar Aliyu Betara ke jagoranta, ya fara bincike a ranar 23 ga watan Disamba.
Kwamitin ya ce zai ƙoƙarin kammala binciken a kan lokaci, tare da gabatar da rahotonsa.