NLC ta sa zare da gwamnati kan kin biyan ma’aikata N35,000 na Cire tallafi

NLC da TUC sun bukaci gwamnati ta gaggauta biyan ma’aikata N35,000 na cire tallafin mai na tsawon watannin da ba ta biya su ba.

NLC ta sa zare da gwamnati kan kin biyan ma’aikata N35,000 na Cire tallafi

Kungiyar Kwadago (NLC da TUC) ta gargadi Gwamantin Tarayya kan kin biyan ma’aikata tallafin N35,000 da ta yi musu alkawari duk wata kan cire tallafin mai.

Kungiyar kwadago ta yi gargadin ne a lokacin da take zargin Gwamnatin Tarayya da saba alkawarin da ta yi na biyan ma’aikata N35,000 na tsawon wata shida domin rage radadin cire tallafin mai.

Shugaban kungiar TUC, Festus Osifo bayyana cewa ma’aikata sun shaida musu cewa sau daya kadai gwamnatin ta biya N35,000 daga lokacin da Shugaba Tinubu ya sanar da matakin.

Ya ce sabanin alkawarin biyan kudin da Tinubu ya yi, a watan Satumba kadai Gwamnatin Tarayya ta aka biya ma’aikatanta kudin, in banda wasu tsiraru da suka samu daga baya.

Da yake magana bayan taron gaggawa da suka yi a Abuja a ranar Talata, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su yi damarar biyan ma’aikata kudaden, kamar yadda gwamnatocin suka jima suna bukatar ma’aikatan da su yi hakuri.