NLC ta umarci ma’aikatan da ba a biya sabon albashi ba su shiga yajin aiki

Ƙungiyar Ƙwadago ta umarci ma’aikata sun fara yajin aikin sai abin da hali ya yi a duk jihohin da ba a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024

NLC ta umarci ma’aikatan da ba a biya sabon albashi ba su shiga yajin aiki

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta umarci mambobinta su fara yajin aikin sai abin da hali ya yi a duk jihohin da ba a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024

NLC ta bayyana rashin biyan sabon mafi ƙarancin albashin a matsayin raina doka da kuma watsi da mawuyacin halin da miliyoyin ’yan Nijeriya suke ciki.

Majalisar Zartarwar NLC ya haƙƙoƙinsu bayyana cewa tsantsar yaudara ce da bautar da ma’aikata, abin da wasu gwamnoni suka yi na kin biyan sabon albashi.

Ƙungiyar ta bayar da umarnin ne baya taron da Majalisar Zartaswar ta gudanar a ƙarshen mako, inda ta yi tir da yadda gwamnoni suka ki biyan ma’aikata haƙƙoƙinsu a yayin da ake ake fama da matsin tattalin arziki a Nijeriya.

Ta bayyana cewa raina doka da tozarta nauyin kare ma’aikata ne gwamnonin suka yi n rashin biyan su sabon albashi.