NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki

NLC ta yi barazanar shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar.

NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki

Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya, NLC, ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin wutar lantarki a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke fama da ƙuncin rayuwa.

NLC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki da masu amfani da layin A da B da C.

Channels TV ya ruwaito wannan daga sanarwa da NLC ɗin ta fitar a ranar Lahadi bayan wani taro da ta yi a Jihar Adamawa.

“NLC ba ta amince da yunƙurin Hukumar Lantarki ta Nijeriya NERC na ƙoƙarin sauya layin lantarkin kwastomomi daga layin B da A da sunan haɓaka samun lantarki ba, alhali kuma yunƙuri ne kawai na ƙara wa mutane kuɗin wuta ba tare da sun shirya ba,” in ji sanarwar.

“Ya bayyana ƙarara cewa dai yanzu masu ƙarfi a ƙasar na ƙara jefa marasa ƙarfi cikin ƙunci ta hanyar ƙara kuɗin haraji da lantarki da sauransu a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya tsaya cak.”

Ƙungiyar ta ƙara da cewa ba za ta lamunci ƙarin kuɗin wutar ba, inda ta yi barazanar shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar.

A makon jiye ne dai Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya sanar da cewa za a mayar da masu amfani da lantarki a sauran layikan zuwa layin A.

Tun a bara ce Gwamnatin Tarayya ta rarraba rukunin biyan kuɗin lantarki aji-aji, inda kowane rukuni zai riƙa biyan kuɗin gwargwadon sa’o’in da yake samun wutar lantarki duk rana

An sake zaɓen Obasa Kakakin Majalisar Legas

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki

HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja

NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki