NLC za ta shiga yajin aiki kan janye tallafin mai

Kungiyar Kwadago ta Najeriya za ta shiga sabon yajin aiki kan janye tallafin man fetur da ya jefa ’yan Najeria cikin kuncin rayuwa.

NLC za ta shiga yajin aiki kan janye tallafin mai

Zanga-zangar NLC

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) za ta shiga sabon yajin aiki kan janye tallafin man fetur da ya jefa ’yan Najeria cikin kuncin rayuwa.

NLC ta sanar da ce yajin aikin gargadin zai fara ne ranar Talata na tsawon kwana biyu.

Wata uku ke nan bayan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye tallafin man, wanda ya yi sanadin ninkuwar farashin litarsa daga N197 zuwa N620.

Tun ranar 29 ga watan Mayu da ya cire tallafin kungiyar ta yi watsi da matakin, wanda ya yi sanadin ninkuwar farashin sufuri da na sauran abubuwa a Najeriya.

NLC ta yi zanga-zanga a fadin Najeriya a kan tsadar rayuwar da janye tallafin man, wanda bayan nan ta yi barazanar fara yajin aiki.

Sai dai ba ta kai ga fara yajin aikin ba shugaban kasa ya gayyace su domin tattaunawa, inda daga bisani suka jingine zanga-zangar da ma yajin aikin.

Karin bayani na nan tafe.

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa