NMC Ta Shirya Gasar Lissafi ga Dalibai Mata A Najeriya

A karin farko a Najeriya, Cibiyar Ilimin Lissafi ta Kasa (NMC) ta shirya gasar lissafi ga dalibai mata da ke azuzuwan karamar Sakandare. Daraktan cibiyarm Farfesa Promise Mebine, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja, inda ya ce an shirya gasar ne domin karfafa wa daliban guiwar nazarin lissafin. An rantsar da sabon shugaban […]

NMC Ta Shirya Gasar Lissafi ga Dalibai Mata A Najeriya

Wasu dalibai kenan a matarantar ‘yan mata ta Shekara dake Kano

A karin farko a Najeriya, Cibiyar Ilimin Lissafi ta Kasa (NMC) ta shirya gasar lissafi ga dalibai mata da ke azuzuwan karamar Sakandare.

Daraktan cibiyarm Farfesa Promise Mebine, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja, inda ya ce an shirya gasar ne domin karfafa wa daliban guiwar nazarin lissafin.

Ya ce a matakin farko, cibiyar za ta zabo dalibai 120 mafiya kwazo daga dukkanin mazabun Najeriya.

“Daga ciki mu sake zabo 20 mafiya kwazo daga kowace Jiha, wadanda da su za a je zagaye na biyu na gasar.

“Sai kuma zagaye na uku wanda za a fitar da wadanda suka fi maki guda uku daga Jihohi daban-daban, mu hada su wuri guda domin zabo wanda ya fi kowa,” in ji shi.

Daraktan ya kuma roki kungiyoyin gida da na kasashen waje, da su hada hannu da cibiyar domin daukar nauyin zakaran gasar.

Ya ce hakan zai sanya gasar koyon ilimi a tsakanin dalibai mata ’yan Najeriya wadanda aka saba barin su a baya a harkar ilimin boko.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano