NNPC babbar matsala ce, a sayar kawai —El-Rufai
El-Rufai ya ce babu amfani gwamnati ta ci gaba da harkar mai, tunda duk abin da yi a bangaren ya gaza
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce Gwamnatin Najeriya ta gaza a bangaren mai da iskar gas, don haka ya kamata ta janye kanta daga bangaren.
El-Rufai ya ce babu amfani gwamnati ta ci gaba da harkar mai, tunda duk abin da yi a bangaren, ciki har da cefanar da NNPC, haka ba ta cim-ma ruwa ba.
- El-Rufai zai gina ‘Film Village’ a Kaduna
- Wayar baturen da ta bace a Ingila ya gano tana Najeriya bayan wata guda
- Makarkashiyar tsige Shugaban INEC ta tayar da kura
“Harafin L da aka kara a sunan NNPC babu abin da ya sauya; har yanzu kudadenmu suke ci, suna cewa an samu riba amma ba mu ga ko sisi ba.
“NNPC babbar matsala ce a Najeriya, wadda dole mu magance ta, in ba haka ba za ta durkusar da kasar nan,” in ji shi, a A jawabinsa a Taron Zuba Jari na Kaduna (KADINVEST).
El-Rufai ya ce, Don haka, “Babu dalilin gwamnati za ta ci gaba da yin harkar mai, ya kamata ta janye tunda ta gaza.”
Gwamnan ya ce duk da cewa shgaban NNPC na yanzu, Mele Kyari yana yin iya kokarinsa, amma kamfanin ya gaza, kuma ya kamata a rufe shi.
Ya ce bangarorin da ke bunkasa a Najeriya babu hannun gwamnati a cikinsu, kamar bangaren sadarwa da nisadi da sadarwa da sauransu.
A sayar da kamfanin NNPC kawai —El-Rufai
Da yake jawabi kan taken taron, ‘Gina Tattalin Arziki Mai Nagarta’, El-Rufai ya ce, duk da matakan da aka dauka a NNPC, “Har yanzu da kudaden haraji ake gudanar da kasar nan.
“Dalili shi ne kudaden tallafin da NNPC ke biya sun lakume abun da bangren mai ke samarwa, saboda haka ya kamata gwamnati ta sayar da kamfanin, ya janye kanta daga bangaren mai.
“Tun 1999 nake wannan magana, lokacin ina shugabantar Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamanti, kuma har yanzu ban canza matsayi ba.
“Sannan gwamnati ta cire kanta gaba daya daga bangaren lantarki ta bar wa ’yan kasuwa ta koma gudanar da bangarorin, za ta samu kudade.”