NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya rage farashin litar fetur zuwa Naira 899 daga N1,020.

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Kungiyar Dillalan Mai ta Najeriya (PETROAN) ta sanar da cewa Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya rage farashin litar fetur zuwa Naira 899 daga N1,020.

NNPC ya rage farashin litar mansa ne kwaki kadan bayan Matatar Mai ta Dangote ta rag farashinta a karo na biyu.

Kakakin Kungiyar PETROAN Joseph Obele a cikin wata sanarwa ya bayyana ragin farashin man na NNPC a matsayin tasirin gasar da aka samu a bangaren man fetur bayan janye hannun gwamnati.

“Ana sa ran hakan zai haifar da gasar farashi a tsakanin ‘yan kasuwar man fetur, wana hakan karuwa ce ga masu amfani da man,” in ji sanarwar PETROAN, tana mai yaba wa matakin.

Sanarwar ta bayyana cewa sauyin farashin ya shafi yankuna ne, a yayin da lita a Legas ya koma N899, a Oghara da Fatakwal da Kalaba N970.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tags