NNPCL na neman Gwamnati ta biya shi bashin tiriliyan 4.71 na shigo da man fetur

Kamfanin NNPCL ne neman Gwamnatin Tarayya ta biya shi bashin Naira tiriliyan 4.71 na kudaden man fetur da ya shigo da shi daga kasashen waje

NNPCL na neman Gwamnati ta biya shi bashin tiriliyan 4.71 na shigo da man fetur

Malam-Mele-Kyari

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ne neman Gwamnatin Tarayya ta biya shi bashin Naira tiriliyan 4.71 da yake bin ta na kudaden man fetur da ya shigo da shi daga kasashen waje.

NNPPCL  ya ce kudaden sun kunshi na haraji da kuma karin da aka samu a farashin man da aka shigo da shi daga watan Augustan 2023 zuwa yunin 2024, a sakamakon tashin Dala.

Ministan Kudi, Wale Edun, ya sanar a haka ne a zaman kwamitin rabon kudaden gwamnatin tarayya na watan yuni a Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito daga takardar bayan zaman.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar karancin man fetur da NNPCL ke faman ganin ya shawo kai a fadin kasar.

Ministan ya kara da cewa shugaban kasa ya da izinin a yi lissafin karin farashin da aka samu a sakamakon karin rashin Dala daga watan Oktoban 2023 zuwa Maris 2024.

A cewarsa, NNPCL ya nemi a kara lokacin amma aka ba shi shawarar cewa sai ya nemi sahalewar majalisar tattalin arziki na kasa.