NNPCL ya fara fitar da iskar gas zuwa China da Japan

Kamfanin Mai Na Najeriya (NNPCL) ya ce ya fitar da gas zuwa ƙasashen Japan da China domin sayarwa. Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye, ya ambato Shugaban Hukumar tace mai na NNPC, Segun Dapo, na cewa hakan na daga shirye-shiryen kamfanin na kasancewa mai samar da nagartaccen makamashi a kasuwannin duniya. Dapo ya ce bangarensa ya samu […]

NNPCL ya fara fitar da iskar gas zuwa China da Japan

The Daqing Oil Field, formerly romanized as “Taching”, is the largest oil field in the People’s Republic of China, located between the Songhua river and Nen River in Heilongjiang province.

Kamfanin Mai Na Najeriya (NNPCL) ya ce ya fitar da gas zuwa ƙasashen Japan da China domin sayarwa.

Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye, ya ambato Shugaban Hukumar tace mai na NNPC, Segun Dapo, na cewa hakan na daga shirye-shiryen kamfanin na kasancewa mai samar da nagartaccen makamashi a kasuwannin duniya.

Dapo ya ce bangarensa ya samu gagarumin hadin kai daga bagarorin kamfanin NNPC na gas da kuma na sufurin jiragen ruwa.

A sakamakon haka, jirgin farko dauke da gas din sayarwa ya bar Najeriya zuwa Japan a ranar 27 ga Juni, 2024.

“A shekarar 2021 NNPC ya fara harkar kasuwancin gas kuma kawo yanzu ya fitar da jirager ruwa sama da guda 20 na gas zuwa yankunan Asiya da turai.

“Hakan zai ba kamfanin damar fadada harkokinsa domin samun kaso mai yawa a bangaren ta yadda zai kara shahara da harkar iskar gas,” in ji Dapo.

Nan da watan Nuwamba, ana sa ran NNPC zai kai jirage sama da biyu na gas zuwa kasuwannin kasahen Asiya, har da kari kafin karshen shekara. (NAN)

Tsarin kasuwancin ya kunshi masu kaya su kai tashoshin jiragen ruwan da ake kebe musu domin kayan da ake bukata a kasunannin duniya.

Sai dai mai kayan ne ke daukar alhalin inshorar kayansa har zuwa lokacin da za su isa inda ake bukatarsu.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna