NNPP ba ta kudin kalubalantar nasarar Tinubu a kotu —Buba Galadima

Jigon ya ce tarihin siyasa ne ke maimaita kan sa a tsakanin Tinubu da Kwankwaso.

NNPP ba ta kudin kalubalantar nasarar Tinubu a kotu —Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya ce jam’iyyar ta ki kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023 a kotu saboda rashin kudi.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Arise kan ganawar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da zababben shugaban kasa, Tinubu a Faransa.

Aminiya ta ruwaito wata ganawa da Tinubu da Kwankwaso suka yi a birnin Paris na kasar Faransa.

Har yanzu dai ba a samu cikakken bayani game da ganawar ba, amma an ce sun tattauna batun gwamnatin hadin kan bangarorin biyu da ka iya haifar da kawancen siyasa tsakanin ‘yan siyasar biyu.

Yayin da yake mayar da martani, Buba Galadima ya ce irin wannan ganawa tsakanin ’yan siyasa ba sabon labari ba ne a siyasar Najeriya.

Ya ce, “Bai kamata taron shugabannin siyasa guda biyu ya jawo wa ‘yan kasa farin ciki irin wannan ba.

“Amma kun san Sanata Kwankwaso ya fafata da zababben shugaban kasa a zaben 2023, inda NNPP ta zo ta hudu.

“Duk da haka, bayan fafatawar, jam’iyya daya ce ba ta je kotu ba duk da cewa mu ne kadai muke da kwararan dalilai na zuwa kotu.

“Tarurrukan neman hadin kan kasa ba wani sabon abu ba ne a siyasar Nijeriya. Ya faru a jamhuriya ta farko tsakanin NCNC da NPC – wato jam’iyyun Azikiwe da Ahmadu Bello.

“Daga baya akwai kuma gwamnatin hadin kan da aka kafa tsakanin NPC da NNDP karkashin jagorancin Cif Samuel Akintola na yankin Yamma.

“Gwamnatin Shagari ta NPP karkashin jagorancin Nnamdi Azikiwe ta yi yarjejeniya da gwamnatin NPN.

“Don haka, tarihi ne ke maimaita kansa, shi ya sa ake bukatar wayar da kan matasa tarihin kasarsu.”

Game da dalilin da jam’iyyar NNPP ba ta garzaya kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu kamar yadda jam’iyyar PDP da LP da sauransu suka yi ba, Buba Galadima ya ce jam’iyyar ba ta da isasshen abin da za ta iya yin hakan.

“Na farko, dole ne mu rubuta cewa PDP ce ta kori Kwankwaso da ni. Don haka da ba za mu yi tsere don kawai mu hana su cin zabe ba.

“Amma kuma mun san cewa zuwa kotu na bukatar kudade masu yawa, wadanda ba mu da su.

“Duk wanda zai je kotu kalubalantar zabe, dole ne ya kasance yana da kudin da bai gaza Naira biliyan biyar ba. Ba mu da kudin da za mu yi hakan,” in ji shi.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja