NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini

NNPP na zargin Kawu Sumaila da wasu ƙusoshin jam’iyyar uku a Kano da cin amanarta.

NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini

Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu ƙusoshin jam’iyyar uku kan zargin cin amanarta.

Sauran waɗanda jam’iyyar kan zargin cin amana sun haɗa da Ali Madakin Gini, Sani Abdullahi Rogo da kuma Kabiru Alhassan Rurum.

A bayanin da ya yi wa manema labaru a ranar Litinin a Kano, shugaban jam’iyyar, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce jam’iyyar ta ɗauki matakin ne bayan samun ƴan majalisar da laifin ayyukan zagon ƙasa ga jam’iyyar.

Dungurawa ya ce ’yan majalisar waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP suna gudanar da ayyuka da suka ci karo da manufofi da ƙudurorin jam’iyyar.

Aminiya ta ruwaito cewa duk waɗanda abin ya shafa ’yan majalisa da ke wakiltar Kano a matakin tarayya.

Kawu Sumaila dai shi ne Sanata mai wakiltar Kano ta kudu, yayin da Ali Madakin Gini ya kasance ɗan Majalisar Wakilai daga mazaɓar Dala.

Sai kuma Sani Abdullahi Rogo wanda ɗan Majalisar Wakilai ne daga mazaɓars Karaye da Rogo da kuma Kabiru Alasan Rurum wanda ke wakiltar mazaɓar Rano, Kibiya da Bunkure.

Dakatarwar da NNPP ta yi wa waɗannan ’yan majalisar na zuwa kwana guda bayan da shugaban jam’iyyar APC a Nijeriya Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa akwai waɗanda ke shirin komawa APC daga NNPP ciki har da ’yan Majalisar Tarayya.

A baya-bayan nan ne Sanata Kawu Sumaila ya jagoranci bikin yaye ɗalibai a jami’arsa inda aka ga fuskokin jiga-jigan APC kamar shugabanta na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril.

Jam’iyyar ta ce ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike kan abin da ya faru domin kamo bakin zaren, sannan kuma NNPP ta ce ƙofa a buɗe take domin tattaunawa duk da dakatar da ’yan majalisar da ta yi.

To sai dai jam’iyyar NNPP ta ce idan waɗanda aka dakatar suka nemi afuwa to ƙofa a bude take domin duba yiwuwar basu dama.

An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina

NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini

Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji

Matar aure ta banka wa mijinta wuta