NNPP ta dakatar da Sakataren Gwamnati da Kwamishina a Kano
Shugaban jam’iyyar ya ce sun ɗauki matakin ne saboda rashin bin umarni da sakataren gwamnatin da Kwamishinan suka yi.
Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Baffa Bichi da kuma Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa ne, ya bayyana haka cikin wani sakon sauti da ya fitar, sannan daga bisani ya tabbatar wa wakilinmu.
- Super Eagles: Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafar Libya ya yi murabus
- An kori Kwankwaso, an ƙone jar Hula a Neja
Ya bayyana cewa sun dakatar da mutane biyun ne saboda rashin biyayya, yin amfani da ofishinsu ba bisa ƙa’ida ba da kuma haddasa rikici a jam’iyyar.
“Muna sanar da cewa mun dakatar da Sakataren Gwamnati, Abdullahi Baffa Bichi da kuma Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol, saboda amfani da muƙamansu ba bisa ƙa’ida ba da kuma rashin biyayya ga jam’iyya.
“Muna gode wa shugabannin jam’iyya a mazaɓarsa da kuma ƙaramar hukumarsu ta Bichi da suka kawo mana ƙorafi a rubuce.
“A matsayinmu na shugabannin jam’iyya, mun zauna mun yanke hukunci cewa wannan shi ne abin da ya fi dacewa har sai mun kammala bincike kan lamarin.”
Aminiya ta ruwaito cewa rikici na ƙara ƙamari tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP a yankin Bichi.