NNPP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Kano baki ɗaya

Jam’iyyar ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar a ranar Asabar.

NNPP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Kano baki ɗaya

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta lashe kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 44 da kansiloli 484 a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ce, ta ayyana jam’iyyar a matsayin wadda ta lashe zaɓen gaba ɗaya.

Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malunfashi ne, ya sanar da hakan da yammacin ranar Asabar.

Ya bayyana cewa KANSIEC ta gudanar da aikinta na gudanar zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Kano.

A cewarsa, an gudanar da zaɓen cikin lumana da nasara.

Ya gode wa hukumomin tsaro, kafofin yaɗa labarai, shugabannin jam’iyyu da al’umma, tare da ƙungiyoyin matasa da mata da suka bayar da goyon baya ga tsarin dimokuraɗiyya.

Ya kuma nuna godiyarsa ga mutanen Jihar Kano bisa goyon bayansu na tabbatar da zaɓen ya gudana cikin lumana.

Jam’iyyu shida ne suka shiga zaɓen na ranar Asabar; AA, AAC, Accord, ADC, APM, da kuma jamiyyar NNPP.