NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC
Yusuf Shitu Galambi. Shi ne ɗan jam’iyyar NNPP na farko da ya sauya sheƙa ya koma APC.

Jam’iyyar adawa ta NNPP ta rasa ɗaya daga cikin mambobinta a Majalisar Wakilai zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram ta Jihar Jigawa, Yusuf Shitu Galambi. Shi ne ɗan jam’iyyar NNPP na farko da ya sauya sheƙa ya koma APC.
Idan dai za a iya tunawa, ’yan jam’iyyar adawa na PDP da LP da dama sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Ɗan Majalisa Galambi ya bayyana cewa, ya bar jam’iyyar NNPP ne saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar wanda ya haifar da wasu ƙararraki da suka shafi ayyukan jam’iyyar.
Ya kuma ƙara da cewa, Jam’iyyar NNPP ta rabu gida biyu sakamakon rigimar mulki tsakanin iyayen jam’iyyar da suka kafa ta, Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso da ɗan takararta na Shugaban ƙasa a shekarar 2023, Peter Obi.