NNPP ta tsayar da Abba Gida-gida takarar gwamnan Kano

An yi masalaha wajen tsayar da Sanata Shekarau da ’yan takarar kujerar sanata da majalisar tarayya da ta jihar Kano

NNPP ta tsayar da Abba Gida-gida takarar gwamnan Kano

Abba gida-gida

Jam’iyyar NNPP ta tsayar da Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida a matsayin dan takararta na Gwamnan Jihar Kano.

NNPP ta kuma bai wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, takarar kai-tsaye domin komawa kujerarsa ta Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya.

Jam’iyyar ta bai wa Sanata Shekarau takarar ce sa’o’i kadan bayan ya sauya sheka zuwa  cikinta daga jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Aminiya ta gano cewa NNPP ta tsayar da Abba Gida-Gida ne a matsayin dan takarar kai-tsaye tare da wanda ya yi mishi takarar Mataimakin Gwamna a zaben 2019, Aminu Abdussalam.

Majiyoyinmu masu tushe a NNPP sun shaida mana cewa jam’iyyar ta kara ba wa Abba Gida-gida da Abdussalamsu dama a 2023 ne lura da irin farin jinin da suke da shi a zaben 2019.
’Yan takarar biyu sun yi tashe kwarai a zaben 2019, musamman da wakar nan ta ‘Abba gida-gida’ amma suka sha kaye a hannun gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje, a zagaye na biyun zaben.

Zaben Abba Gida-gida da Ganduje ya tayar da kura matuka, kuma shi ne na farko da fara zama ba a kammala ba a Najeriya.

Takarar majalisa: NNPP ta yi masalaha a Kano

Sauran wadanda jam’iyyar ta ba wa takarar ta hanyar masalaha a Jihar Kano sun hada da tsohon Babban Sakataren Asusun Kula da Jami’o’i ta Najeriya (TETFund), Abdullahi Baffa a kujerar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa.

Shi kuma tsohon dan Majalisar Wakilai, Honorabul Abdulrahman Kawu Sumaila, shi ne ya zaman dan takarar kujerar Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu.

An kuma bai wa sabbin shiga jam’iyyar irin su tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhassan Rurum, takarar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kibiya/Bunkure/Rano.

Tsohon dan Majalisar Wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya samu takarar kai-tsare domin komawa kan tsohuwar kujerarsa ta mazabar Kiru/Bebeji.

Shi ma Tijjani Abdulkadir Jobe, an ba shi takarar kujerar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Dawakin Tofa/Tofa/Rimingado ta hanyar masalaha.

Aminiya ta kuma ga jerin sunayen ’yan takara 36 cikin mutum 40 da NNPP ta yi masalaha a kansu a kujerun Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50