NNPP ta yi martani kan alkalan da suka yanke hukuncin zaben Kano

Masu jajayen huluna sun kore mu daga Kano

NNPP ta yi martani kan alkalan da suka yanke hukuncin zaben Kano

NNPP

Babban mai binciken kudi na jam’iyyar NNPP ya caccaki alkalan da suka yi hukuncin shari’ar zaben gwamnan Kano bisa kalaman da suka yi game da jam’iyyar da ’ya’yanta.

A wata sanarwa da Ladipo Johnson ya fitar, ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda alkalan suka yi amfani da ‘munanan kalamai’ a kansu a lokacin da suka yi hukuncin da ya bai wa Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC nasara.

A hukuncin da alkalan suka yi a Larabar makon jiya, Mai Shari’a Benson Anya ce “Ina amfani da wannan damar domin yin tir da gungun masu jajayen huluna wadanda ke kama da ‘yan ta’adda, inda suka kore mu daga Kano tare da saka rayukanmu cikin fargaba.

“Mun yi amannar cewa Allah kadai ke ba da mulki.

Sai dai a martanin da jam’iyyar NNPP ta mayar, ta ce wadannan kalaman ba su dace a ce sun fito daga alkali kuma mai kare doka ba.

“Ba shakka, kalaman batanci da cin mutunci da tsinuwa da Mai Shari’a Benson Anya ya yi sun wuce ka’idojin shari’a, hakan ya nuna alamun yana da ra’ayin wata jam’iyya sakamakon yadda yake nuna kyama ga shugabanni da mambobin NNPP.

Ya jaddada cewa jam’iyyar NNPP za ta dauki matakan da suka dace wadanda suka hada da gabatar da korafi kan alkalan a Hukumar Kula da Alkalai ta Najeriya kan kalaman da alkalan suka yi da kuma daukaka kara kan hukuncin da alkalan suka yanke wanda ya cire Abba Kabir Yusuf daga gwamna.

Ya jaddada cewa suna da karfin gwiwa kan cewa za a yi musu adalci a Kotun Daukaka Kara don karfafa imanin mutane a bangaren shari’a da dimokuradiyya.

Aminiya ta ruwaito cewa, kwanaki kadan kafin yanke wannan hukuncin, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sallami kwamishinansa Adamu Kibiya sakamakon barazana ga alkalan da ke sauraron shari’ar gwamnan jihar.

‘Masu jajayen huluna sun kore mu daga Kano’

Bayanai sun ce alkalan da suka yi shari’ar zaben Kano sun yi raddi dangane da kalaman da wasu ‘yan jam’iyyar NNPP a jihar suka yi gabannin yanke hukuncin da ya bai wa Gawuna nasara.

A cikin wata takarda na hukuncin da alkalan suka karanto a shari’ar da aka gudanar a ranar Larabar makon jiya ta manhajar Zoom, daya daga cikin alkalan da suka yanke hukunci Mai Shari’a Benson Anya ya caccaki ‘yan Kwankwasiyya.

A yayin da yake karanto hukuncin shari’ar zaben, ya ce bai kamata saboda jita-jita na yawo kan cewa ba za su yi nasara a kotu su rinka barazana ga alkalai ba.

“Kuskure ne a razana siyasar Kano baki dayanta da tarzoma. Kada jam’iyya ta kuskura ta yi wa jama’a barazana da ta’addanci da tashin hankali.

“Kada a dauki hukuncin kotu da zafi wanda har zai sa a kai hari kan ma’aikatan kotu, kamar yadda wakilan wadanda ake kara na biyu da na uku suka yi,” in ji Mai Shari’a Anya.

“Ina amfani da wannan damar domin yin tir da gungun masu jajayen huluna wadanda ke kama da ‘yan ta’adda, inda suka kore mu daga Kano tare da saka rayukanmu cikin fargaba. Mun yi amannar cewa Allah kadai ke ba da mulki.

“Dole wadanda suka yarda da Allah su amince da hakan da kuma mubaya’a ga karfin gwamnati,” in ji shi.

Ya bayyana cewa daukar doka a hannu da tayar da tarzoma ba zai taba zama wata hanya ta samun karfin iko ba.

“Yi wa rayukan alkalai barazana kamar yadda wasu fusatattun barayi wadanda suke kiran kansu ‘yan siyasa suka yi abin takaici ne,” in ji shi.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano