NNPP za ta daukaka kara kan hukuncin kotun kan zaben Kano
Jam’iyyar NNPP za ta daukaka kara domin kalubalantar hukuncin kotun da ta soke zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf
Bayan fitowa daga kotu, lauyan jam’iyyar NNPP, Bashir Muhammad Tudun Wuzirci ya ce hukuncin ya zo musu da mamaki, domkin ya saba da abin da ya kamata.
- Soke zaben Abba: ’Yan kasuwa na rufe shaguna saboda fargabar rikici
- Nasiru Gawuna ne ya ci zaɓen gwamnan Kano —Kotu
Lauyan ya ce NNPP za ta daukaka kara zuwa kotu na gaba kuma suna da kwarin gwiwar cewa kotun daukaka kara za ta warware abin da ya kira “surkullen da aka yi wanda bai kamata a yi ba.”
Baritsa Tudun Wuzurci ya ce kafin tafiya kotu na gaba za su tattauna da wadanda yake wakilta domin daukar matakin da ya dace.
Kotun ta soke nasarar zaben Abba Kabir Yusuf ne bisa cewa shi ba dan Jam’iyyar NNPP da ya yi wa takara ba ne, sannan soke kuri’u 165,663 marasa sitamfin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da aka kada masa, bisa cewa ba halastattu ba ne. Hasali ma, wadannan abubuwa biyu sun saba dokar zabe ta 2022.
Soke kuri’un ya sa addakin kuri’uns yin kasa da na Gawuna, wanda kotu ta umarci INEC ta ba wa takardar shaidar lashe zabe ta kwace wanda ta ba wa Abba da farko.
Da haka kuri’u 1,019,692 da Abba ya samu suka koma 853,939, a yayin da Gawuna mai kuri’u 890, 705 ya sha gabansa da kuri’u 36,766.
Lauyan NNPP ya ce irin haka ta faru a Jihar Osun, amma kotun ɗaukaka ƙara ta zo ta warware kuma Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa abin da tirabunal ta yi ba daidai ba ne.