Noma a wurina sana’a ce ba neman suna ba – Kulu Namani Kotoko
Hajiya Kulu Abdullahi, babbar ’yar shahararren manomin nan marigayi Ali Namani Kotoko kuma ita ce ta gaje shi a harkar noma duk da cewa mace ce. Aminiya ta zanta da ita kan noma da nasarar da ta samu da kuma burinta: Aminiya: Wace ce Kulu kuma yaya aka yi kika tsinci kanki a cikin […]
Hajiya Kulu Abdullahi, babbar ’yar shahararren manomin nan marigayi Ali Namani Kotoko kuma ita ce ta gaje shi a harkar noma duk da cewa mace ce. Aminiya ta zanta da ita kan noma da nasarar da ta samu da kuma burinta:
Aminiya: Wace ce Kulu kuma yaya aka yi kika tsinci kanki a cikin harkar noma?
Hajiya Kulu: Sunana Kulu Abdullahi, an haife ni a garin Wasagu. Ni ce ’ya ta farko a wajen mahaifina marigayi Ali Namani Kotoko. An kai ni wajen yaye a wurin wata Bayarbiya aminiyar mahaifanmu, wata rana za ta je da ni garinsu na Ogbomosho sai muka yi hadarin mota a Bade ta rasu, wannan ne ya sa na dawo wajen mahaifana. Na dawo ba na jin Hausa a lokacin, a haka sai aminin mahaifina ya ce a sanya ni a makarantar boko don idan na hulda da yara ’yan uwana zan koyi Hausa. Da aka sa ni karatun kuwa, sai na dage har na kai ga karatun digiri a Jami’ar Usaman dan Fodiyo a fannin Tarihi. Na yi aure inda na auri Malam Audu Zuru wanda a yanzu shi ne Farfesa Abdullahi Zuru kuma shi ne Shugaban Jami’ar Usman dan Fodiyo a yanzu. Da muka fita kasar waje da mijina, sai na dakatar da noma, bayan mun dawo sai na fada wa mahaifina ina son in koma noman sai yake ce min Kulu noma ba naki ba ne, lokacin ban fahimce shi ba, sai daga baya, domin gwamnati ba ta taimaka wa manoma, ba su kuma samun kwarin gwiwa. Za ka ga manomi ya yi noma ba riba sai hasara, ba a bai wa bangaren muhimmanci, kai za ka samo abinka dole ka samo shi cikin tsada, in za ka sayar ka samu hasara. A lokacin da na dawo noman, mahaifina ba ya da lafiya, bayan ya rasu ne a shekarar 2014 da muka debo amfanin gona ya zama mun yi hasara sosai. Sai kannensa suka ce mu bar noman, ni kuwa na ce musu ba zai yiwu ba, sunan da mahaifinmu ya yi a noma da yadda yake son bangaren a zuciyarsa, kuma ya fada mana ko bayan ransa mu rike noma sana’a. Da muka ci gaba ne muka yi sa’a gwamnati ta juyo kan harkar sai na tabbatar noma sana’a ce domin duk babu abin da za ka yi ka ci riba kamarsa, kuma ina noma ne don ina son kada a manta da sunan mahaifina.
Aminiya: Mene ne sirrin shahararki?
Hajiya Kulu: Muna da bambanci da mahaifinmu, shi ya yi noma ne saboda suna, mu ko muna yi ne saboda riba. Don haka dole ne mu kula da wasu abubuwan da dama. A maganar shahara kuwa a gaskiya ina ganin abin da ya burge mutane game da ni a Kebbi bai fi kasancewata mace ba, na tabbata akwai manoma da ban taka sawunsu ba, amma dai suna mamakin yadda mace ke noman da nake yi. A bara na samu buhun masara da dawa 259 a wata gona kuma 522 (jimilla 781), ban samu shinkafa ba don buhu 15 kawai na yi sabanin 32 da na samu a baya. Gona kuma ina noma mai girman hekta 18 da mai girman hekta 102 da na gada a wurin mahaifina cikin gonarsa mai hekta 500 da muka gada. Sai fadama mai hekta 52. A duk lokacin da za mu fara aikin gona bayan masu gadi, mukan dauki mutum 50 don shuka da noma da sanya taki. A sabon salon da muke amfani da shi kuma mutum ashirin zuwa ashirin da biyar sukan yi fiye da kwana 10 suna aikin haka da girbi, aikin akwai kalubale saboda ba mu da injuna da tasirinsa ya fi haka.
Aminiya: Ana cewa lokacin kina karama duk wani mabukaci in ya zo wurin mahaifinki neman tsaba ke yake kira ya sanya kanki a masaki tsaba ta zubo, ba sai ya debo a rumbu ba, mene ne gaskiyar wannan zance?
Hajiya Kulu: Ba zan iya tuna wannan ba gaskiya. Abin da zan iya fada kawai shi ne mahaifinmu mutum ne mai kwazon aiki, kuma jarumi ne, ba ni kadai ce na gaje shi ba, ni kadai ce dai aka fi sani don ya ba mu tarbiyyar hadin kai ta yadda ba wanda zai iya raba kanmu. Kuma kasancewa ni ce babba akwai girmamawa, duk abin da na ce ba a musu.
Aminiya: Ko kina da wani shiri na canja tunanin mata su shigo harkar noma gadan-gadan?
Hajiya Kulu:Abin da nake fatan gani shi ne maza da hukuma su bai wa mata goyon baya a taimaka musu da tallafi, idan an cire amfanin gona sai su biya ko a raba riba. Ina da shirin da zan fito da shi da kudina don taimaka wa mata su yi noma a san su ma za su iya. Ya kamata gwamnati ta yi yekuwar mata su yi noma domin addini ya bai wa mata damar su yi sana’a sai kuma a ba su kwarin gwiwa da kulawa don ita ce na samu. Mahaifinmu ya bar mana kasa da tarbiyya shi ne ya sanya mutane ke cewa Namani bai mutu ba.
Ga shi mun kara samun daukaka, gwamnati ta daraja noma sosai duk da cewa sai a bana ne gwamnati ta san da ni ta ba ni tallafin noman rani na iri da taki da injin ban -ruwa, gaskiya shirin tallafa wa manoma bai yi tasiri ba sosai, domin daga baya na ji an ce irin anko baya da kyau na alkama kuma ba a bayar cikin lokaci ba. Amma dai ba komai manoma sun koya ne, idan na samu irin zan shuka shi duk da ina tanadar nawa mai inganci. Ina kira ga nanoma kamar yadda muka riki noma sana’a, mu karbi canjin da ke zuwa don gwamnati na nufin mu rika dogaro da namu mu fita batun na waje.