Noma ba taki wahala

A bana ma, kaman ‘yan shekarun baya, damina ta sauka akan kari, kuma a halin yanzu kusan dukkan  kusurwowin  lungunan yankin Arewacin kasar nan sun samu ruwan  farko, manoma kuma sun shuka amfani. Amma sai dai abin mamaki, ko kuma a ce takaici game da haka shi ne yadda hukumomi ba su damuwa da faduwar […]

Noma ba taki wahala
Noma ba taki wahala

A bana ma, kaman ‘yan shekarun baya, damina ta sauka akan kari, kuma a halin yanzu kusan dukkan  kusurwowin  lungunan yankin Arewacin kasar nan sun samu ruwan  farko, manoma kuma sun shuka amfani. Amma sai dai abin mamaki, ko kuma a ce takaici game da haka shi ne yadda hukumomi ba su damuwa da faduwar damina, balle har su tashi haikan wajen fadakar da manoma fa’idojin yin harama ko kuma samar masu da kayayyakin da suka wajaba bayan faduwar daminar. Abin da kawai hukumomi suka fi zakewa akai a ‘yan shekarun nan shi ne batun ambaliyar ruwan da ke addabar birane da kauyuka.
Ba makawa ambaliyar ruwa babban bala’i ne kuma wajibi ne a tashi haikan wajen fadakar da jama’a don gujewa illolin da yake haddasawa. To idan  da  a ce yadda jami’an hukumomi ke yin zumudi game da batun ambaliya, haka nan kuma suke fadi-tashi wajen fadakar da manoma  game da yanayin  damina da dabarun sharar gona tun kafin  faduwar  ruwan sama da kuma taimaka masu da ingantaccen irin shuka da maganin karkashe kwari  da wadataccen takin zamani, nau’uka iri-iri, ai da ba haka ba. Kazallahar da suke yi wajen damuwa game da batun ambaliyar ruwa don sun san cewa akwai abin da suke kankara ne daga cikin kudade da kayayyakin agajin da gwamnatoci kan bayar ga wadanda suka tagayyara.
Irin wannan hali na shugabanni ne ke karya gwiwowin manoma a dukkan lokutan da suka bukaci tallafi ko agajin gaggawa daga wajen hukumomi don kyautata harkokin noma. A takaice dai, ya zuwa yanzu, an samu watanni biyu da yin shuka a wasu sassan, amfani ya fito, an yi noman farko, wasu ma sun yi mai-mai, ba tare da sun samu takin da gwamnati kan sayar masu ba. Dalili kuwa shi ne sai bayan faduwar damina ce sa’annan aka san cewa manoma za su bukaci taki don amfanin da suka shuka, kuma a lokacin ne za a kukuta don sayowa daga kasashen ketare.
Ba wanda bai san cewa ba domin amfanin manoman ne ba ake  shigo da takin zamanin, sai dai don amfanin wasu ‘yan tsiraru ne can dabam, wadanda ba ruwansu da noman. Kuma don haka ne ake bari sai bayan damina ta yi nisa sannan a samar da shi ta hannun jami’an gwamnati da hamshakan ‘yan siyasan da za su yi dillancinsa ga manoma kan farashi mai dan karen tsada. Idan har gwamnati na kashe makudan kudade wajen sayen takin zamani, kuma hakan bai sanya takin na samuwa ga manoma cikin sauki da rahusa ba, to akwai babbar matsala game da haka. Shi ya sa manoma da kuma talakawan da ake yi dominsu ba su amfana da komai, haka nan  suke tashi a tutar babu.
Wannan ne ya sa kananan manoma ba su iya noma amfanin da za a sayar don raya  manya da kananan masana’antun kasar nan; iyakansu samar da hatsi don amfanin iyalansu, kuma cikin watanni uku sun cinye, kafin zagayowar kaka sai sun hada da awo. Dangane da haka masana’antunmu suka ruguje sakamakon rashin amfanin gonan da za su sarrafa domin manoma ba su iya nomawa saboda ba riba. karfi da yaji an daina noman raken da za a mayar sukarin da muke tsananin bukata a kullum; ba mai noman alkamar da za a sarrafa don yin burodi ko makaroni ko kuma taliyar da suka fi karfin talaka. Da gangar kuma aka janye hankalin manoma daga noma shinkafa ‘yar gida, sai dai ta waje, wacce ta zama cimakar talaka da masu hali, kowane gida ita ake dafawa  da rana, ita kuma ake tukewa da daddare.
Shi ya sa a kowace shekara ake kashe makudan kudade sama da Naira biliyan dari tara da sittin N960b wajen sayen shinkafa da alkama da sukari har ma da man gyadar da aka noma a kasashen  ketare. Wato dai  ba mu isa mu ciyar da kanmu ba sai dai a ciyar da mu, duk kuwa da kasar noma mai albarka da muke da ita a kasar nan da  kuma matasa majiya karfi da za su dukufa noma dukkan nau’in albarkatun abinci da na masana’antu da kasar ke bukata.  Ya zamanto dole a noma su a wasu kasashe, a kawo mana, mu saya, shugabanninmu suna ji, suna gani, ba za su dauki matakan hana shigo da  kayayyakin abinci daga ketare wadanda ke kashewa na cikin gida kasuwa.  To tun da shugabanni na amfana da dan kalilan daga cikin dimbin dukiyar da ake fitarwa kowace shekara don sayo abinci daga ketare, me zai dame su idan  manoman wadancan kasashen suna amfana maimakon ‘yan kasarsu?
A fadin Afirka, kafatan, babu wata kasa kamar Najeriya mai dimbin albarkatu da ma’adinai da yawan bil-adama, kuma wadannan sun isa a ce ita ce kan gaba wajen samar da abinci don ciyar da dimbin jama’ar cikinta da samar da dukkan albarkatun gonan da masana’antu ke bukata  a nan cikin gida, a kuma fitar da ragowar zuwa wasu kasashe don sayarwa. Amma, kash! Wadannan albarkatu ba su da fa’ida ga jama’an kasar don ba su cin moriyarsu, wasu ne can dabam ke amfana daga gare su. Idan da ba haka ba ai da Najeriya ta wadatu da masana’antu, manomanta sun zame manyan attajirai Ba wani abu ba ne kuwa ya jawo haka illa sakacin da shugabanni suka yi da noma a matsayinsa na almakashin yanke talauci, suka bar talaka da wahalar banza wajen noma ba taki.