Noma ba taki wahala 01

A bana ma, kamar ‘yan shekarun baya, damina ta sauka akan kari, kuma a halin yanzu kusan dukkan  kusurwowin  lungunan yankin Arewacin kasar nan sun samu ruwan  farko, manoma kuma sun fara  shuka amfani, wasu na jira isowar  daminar. Amma sai dai abin mamaki, ko kuma a ce takaici game da haka shi ne yadda […]

Noma ba taki wahala 01
Noma ba taki wahala 01

A bana ma, kamar ‘yan shekarun baya, damina ta sauka akan kari, kuma a halin yanzu kusan dukkan  kusurwowin  lungunan yankin Arewacin kasar nan sun samu ruwan  farko, manoma kuma sun fara  shuka amfani, wasu na jira isowar  daminar. Amma sai dai abin mamaki, ko kuma a ce takaici game da haka shi ne yadda hukumomi ba su damuwa da faduwar damina, balle har su tashi haikan wajen fadakar da manoma fa’idojin yin harama ko kuma samar musu da kayayyakin da suka wajaba bayan faduwar daminar, rashin yin haka kan kari ne musababin afkuwar matsalolin da manoma kan ci karo da su da zarar  daminar ta sauka.
Ba makawa matsalolin da kan yi wa damina rakiya da batun ambaliyar ruwa matsananta  ne, kuma wajibi ne a tashi haikan wajen fadakar da jama’a don guje musu. To idan  da  a ce yadda jami’an hukumomi ke yin zumudi game da batun ambaliya, haka nan kuma suke fadi-tashi wajen fadakar da manoma  game da yanayin  damina da dabarun sharar gona tun kafin  faduwar  ruwan sama da kuma taimaka musu da ingantaccen irin shuka da maganin kashe kwari da wadataccen takin zamani, nau’uka iri-iri, ai da ba haka ba.
Irin wannan hali na shugabanni ne ke karya gwiwowin manoma a dukkan lokutan da suka bukaci tallafi ko agajin gaggawa daga wajen hukumomi don kyautata harkokin noma. A takaice dai, ya zuwa yanzu, manoma sun kimtsa kaf don fara aikin gona a wannan shekarar. Sun share gonakinsu fes, sun tanadi takin kashin dabbobi da dattin jujin gidajensu, sun kuma adana  ingantaccen irin da za su shuka da zarar damina ta  kankama, amma babu  takin da gwamnati kan sayar musu, kuma babu wata gwamnati a yankin Arewa da ta  za ta bugi kirji, ta ce ta tanadi wadataccen takin da manoman jiharta ke bukata kafin faduwar damina.Sai bayan damina ta  yi zurfi, amfanin da aka shuka ya yi  yabanya,  har yana jan-kara, sa’anan  za a kukuta, a nemi sayo takin kasashen ketare, kuma kafin ya zo amfanin ya fara sauya launi, yana  yin ja-ja, ko ma ya  yankwane gaba daya.
Ba wanda bai san cewa ba domin amfanin manoman ne ba ake  shigo da takin zamanin, sai dai don amfanin wasu ‘yan tsiraru ne can daban, wadanda ba ruwansu da noman. Kuma don haka ne ake bari sai bayan damina ta yi nisa sannan a samar da shi ta hannun jami’an gwamnati da hamshakan ‘yan siyasar da za su yi dillancinsa ga manoma kan farashi mai dan karen tsada. Idan har gwamnati na kashe makudan kudi wajen sayen takin zamani, kuma hakan bai sa takin na samuwa ga manoma cikin sauki, kuma da   rahusa, to akwai babbar matsala game da haka. Shi ya sa manoma da kuma talakawan da ake yi dominsu ba su amfana da komai, haka nan  suke tashi a tutar babu, ko kuma a ce hannu-rabbana.
Wannan ne ya sa kananan manoma ba su iya noma amfanin da za a sayar don raya  manya da kananan masana’antun kasar nan,  iyakarsu samar da hatsi don amfanin iyalansu, kuma cikin watanni uku sun cinye, kafin zagayowar kaka sai sun hada da awo. Dangane da haka masana’antunmu suka ruguje sakamakon rashin amfanin gonar da za su sarrafa, domin manoma ba su iya nomawa saboda ba riba. karfi da yaji an daina noman raken da za a mayar sukarin da muke tsananin bukata a kullum; ba mai noman alkamar da za a sarrafa don yin burodi ko makaroni ko kuma taliyar da suka fi karfin talaka.
Da gangan kuma aka janye hankalin manoma daga noma shinkafa ‘yar gida, sai dai ta waje, wacce a yanzu ta zama cimakar talaka da masu hali, kowane gida ita ake dafawa  da rana, ita kuma ake tukewa da daddare. Abin har ya kai ‘ya’yanmu ba su son wani abinci sai shinkafa ‘yar waje da miyar dage-dage, ko a yi dafa-dukanta, yara suna ci, suna wakar rengen, rangen-gen.
Wannan sabuwar gwamnatin canji ta APC ta yi alkawarin habaka aikin gona, musamman ma don a rage dogaro daga abincin da ake sayo wa daga ketare, ta yadda makudan kudin sayowa  za su dinga shigewa aljiffan manoman kasar nan. An fahimci cewa da gaske take yi domin kuwa ga shi nan ta ware wasu Naira miliyan dubu 20 don habaka aikin shinkafa a Jihar Kebbi, kuma wasu hamshakan ‘yan kasuwa da ke jigilar shigo da ita daga ketare sun fara narkar da dukiyarsu don noman shinkafar a nan cikin gida.
A fadin Afirka, kafatan, babu wata kasa kamar Najeriya mai dimbin albarkatu da ma’adinai da yawan bil-adama, kuma wadannan sun isa a ce ita ce kan gaba wajen samar da abinci don ciyar da dimbin jama’ar cikinta da samar da dukkan albarkatun gona da masana’antu ke bukata  a nan cikin gida, a kuma fitar da ragowar zuwa wasu kasashe don sayarwa, daidai da manufar sabuwar Gwamnatin Muhamadu Buhari.Hakan shi ne mafita daga matsalar karayar arzikin da ya gallabi Najeriya a halin yanzu, ake kuma neman a tayar da komada ta hanyar  raja’a ga aikin gona gadan-gadan, don talakawa su ci moriyar taimako da tallafin da gwamnati za ta bayar, wasu can su daina amfana daga abin da za mu iya samarwa da kanmu. Yin haka ne kawai zai sa Najeriya ta wadatu da masana’antu, manomanta su zame manyan attajirai da hamshakan ‘yan kasuwan  da za su yi dillancin amfanin kasarsu can a kasashen makwabta, maimakon yadda a ‘yan shekaru aka mayar da kasarsu kasuwar kayayyakin da aka noma a wasu kasashen ketare, ake kawo wa don ciyar da su.  Ba wani abu ba ne kuwa ya jawo haka illa sakacin da shugabanni suka yi da noma a matsayinsa na almakashin yanke talauci, suka bar talaka da hauma-hauma, har  sai da ya fahimci cewa noma ba taki dai babbar wahala ce.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos