Noma da kiwo sun fi fetur inganta tattalin arziki
Tattalin arzikin kasa shi ne irin ma’adanai da ke jibge a karkashin kasa ko samanta da sarrafa wadannan ma’adanai don gina kasa da ’yan kasa. Allah Ya albarkaci Najeriya da kusan dukkan ma’adanai da kasashe ke iya gadara da su, kama daga Man-Fetur da Iskar Gas, Kalanzir, karfe da tama da karfen kuza da dai […]
Tattalin arzikin kasa shi ne irin ma’adanai da ke jibge a karkashin kasa ko samanta da sarrafa wadannan ma’adanai don gina kasa da ’yan kasa. Allah Ya albarkaci Najeriya da kusan dukkan ma’adanai da kasashe ke iya gadara da su, kama daga Man-Fetur da Iskar Gas, Kalanzir, karfe da tama da karfen kuza da dai sauransu. Amma wadannan duk ba su ne muhimman sinadaran tattalin arziki da ya kamata kasa ta yi gadara da su ba. Abubuwan da suka kamanci a yi gadara da su su ne, noma da kiwo.
Idan muka yi duba ga kasashen duniya mafi karfin tattalin arziki, za mu ga cewar idan ba dukkansu ba, mafi yawan su, ba su damu da duk wadannan ma’adanai da suke da su ba, wasunsu ma ba su da su balle su yi amfani da su. kasashe irin su Amurka da Brazil da Sin (China), Indiya, Indonusiya da Jamus, sun dogara ne kacokan kan arzikin noma, yayin da suka yi fice wajen sayer da shinkafa, alkama da masara ga kasashen duniya irin su Najeriya.
kasashen kungiyar OPEC masu fitar da man-fetur mafi yawa a duniya, wadanda suka hada da Aljeriya da Angola da Ekodo da Iran (Farisa) da Kuwaiti da Libya da Najeriya da Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa da benezuela, kusan dukkanin wadannan kasashen ba su iya noma abin da za su ci sai sun sayo abinci irin su shinkafa da alkama daga kasashen waje, kamar su Amurka da Brazil.
A shekarar nan da muke ciki (2014), Gwamnatin Najeriya ta yi shelar karuwar karfin tattalin arzikinta, (wato Gross Domestic Product) wanda ya kai Dala biliyan 502 (Kimanin triliyon N80.5) a karshen shekarar 2013. Haka zalika, a shekarar 2012 ne ma’aikatar kididdiga ta (National Bureau of Statistic) ta ce sama da kashi 70% na mutanen Najeriya su na rayuwa ne a cikin matsanancin talauci duk da cewar Najeriyar itace ta 8 acikin jerin kasashen OPEC masu fitar da Man-fetur mafi yawa a duniya.
Kamar yadda kididdiga ta nuna a shekarun baya da suka wuce, noma da kiwo su ke da sama da kashi 70% na tattalin arzikin Najeriya (daga Dalar gyada da kwakwar manja da auduga, Shanu da sauran su), amman a yau Man-fetur ne ya mamaye tattalin arzikin da kusan Kashi 95.3% (Shekara, 2010). Wannan ta sa shigowa da abinci Najeriya irin su Shinkafa, Siga, Nama, Kifi da Madara ke ta karuwa da kashi 36.7% tin daga shekarar 2011 zuwa yau (Jaridar banguard ta ranar 6/2/2013).
An kiyasta cewar, Man-fetur din da ke jibge a Najeriya bai wuce ganga biliyan 37,200 ba, kuma zai iya karewa zuwa wadansu shekaru masu zuwa (Inji dandalin Wikipedia). Idan muka dauki misali tsakanin Man-gyada da Man-fetur, za mu ga cewar gidan kowanne talaka ana amfani da man-gyada, amma ba kowane gida ne ake amfani da man-fetur ba. Kuma lita daya ta man-fetur din ba ya wuce N97 zuwa N120 amma lita daya ta man-gyada takan kai har N250, kuma har ila yau man-gyada baya fuskantar barazanar karewa kamar na man-fetur.
Arewacin Najeriya ce ke da filin noma da kiwo, a cikin duk tafiyar mil 100 da mutum zai yi a Arewa, mil 60-70 filin noma da kiwo ne babu gari. Har ila yau, Arewan ce ke da tafkuna irin su tafkin Chadi da Chalawa, Tiga da Rima da koguna da suka ratsa daukacin yankin wanda ke dauke da filayen noma da kiwo .Jihohi irin su Kano da Kaduna da Borno da Benue da Adamawa da Filato da Taraba kawai, za su iya noma shinkafa da doya da alkamar da mutanen Najeriya za su ci a shekara idan aka kula da bada taki da iri mai kyau akan lokaci.Haka zalika in muka koma kiwo, babu wata Jihar Arewacin Najeriya da babu wuraren kiwo (wato Lawani). Samar da Nama da Fata da Kashi da gashi da da duk wani abin da ake bukata daga Saniya, Akuya/Tunkiya, Rakumi, Kaji/Zabi ko Kifi sai a yankin Arewacin Najeriya.
Amman abin mamakin shi ne, wadansu abokan zaman mu a Najeriya (daga yankin kudanci) na kiran mu da cima-zaune, ma’ana mu ‘yan arewa bama tallafa wa Tarayyar Najeriya da komai na kudin shiga kamar yadda Neja/Dalta ke yi, wannan kuwa ya farune don shugabannin mu na arewa sun gagara kyautata ayyukan noma da kiwo a yankin namu, sun bar al’amurran kudin shigar su daga albarkatun man-fetur kawai. Don haka nema wasu daga cikin su ke kiran a raba Najeriya don su a ganin su, yunwa ma za ta kashe mu idan aka rabu, domin ba mu da man-fetur a yankin mu. Amman sun manta da cewar, duk wani tumatiri da albasa da tattasai da attaruhu da naman saniya da akuya da tunkiya, daga wurin mu ake kai musu.
Duk da cewar man-fetur yakawo ci gaba, amman kusan za a ce namai tonon rijiya ne. Kafin samun man-fetur a Najeriya, babu cinhanci da rashawa, babu nuna bangaranci, kabilanci ko kungiyoyi masu fada da Gwamnati akan man-fetur, amman yanzu duk wadannan sun zama ruwan dare. A wancan lokacin, abinci bai gagari talaka ba, domin zai iya noma abin da zai ci a gonarsa, amman yau kowa ya koma sa rai a ayyukan gwamnati ko kamfanoni, anyi watsi da noma balle kiwo dalilin ko-in-ku
Siyasa, bangaranci da kabilanci, da wariyar addini sun taimaka wajen yin ko-in-kula da bangaren noma da kiwo musamman daga gwamnatin tarayya, irin hakan ta faru a kasafin kudin 2014 na gwamanatin tarayya yayin da za ta kashewa tsagyerun Neja/Dalta biliyan N35 amman kuma, aka warewa bunkasa tattalin arzikin Arewa maso Gabas biliyan N2 kacal, yankin da ya kunshi jama’a sama da miliyan 19 (kidaya, 2006).
Abinda nake so jama’a su fahimta anan shi ne, Noma da Kiyo su ne tattalin arzikin da kowace kasa take la’akari da su. Domin dukkanin kasar da ba za ta iya ciyar da kanta ba, tofa ba ta kai a kirata kasa mai cin gashin kanta ba.
Kiraye-kirayena ga dukkanin matakai na gwamnatocin kasannan su ne, inganta harkokin noma da kiwo za su kara kudaden shiga kuma su samarwa talakawa ayyukan yi. Samar da ingantaccen iri da taki akan lokaci, koyar da kiwon kaji, kifi, shanu, awaki da tumaki wa talakawa zaiyi matukar rage radadin talauci, samar da basuka wa al’umma don harkokin noma da kiwo, samar da isassun masana akan harkokin noma don ilimantar da al’umma akan noma da kiyo, samar da kamfanonin sarrafa kayan gona irin su kamfanin tumatir, da dai sauran hanyoyin da suka dace don inganta wannan sashin, zai kara arziki ga kasa, ya rage talauci da kimanin kashi 70%, ya kuma kawo zaman lafiya da cigaban kasa kamar yadda akace ‘ NOMA TUSHEN ARZUKI.
Fatana dai shi ne mu sani cewar, koda zamantakewar mu ta kare da masu man-fetur, to mune muke da dawwamammen tattalin arzikin da za mu rike kanmu da shi, wato ‘Noma na duke tsohon ciniki…….’, kuma dole su yi kasuwanci da mu wajen sayen dabbobin mu da kayan masarufin mu tun da ba a shan man-fetur.
Allah ya taimaki kasar mu Najeriya, amin.
Salisu H. Dango, Yana, K/H, Jihar Bauchi [email protected]
2348032875677