Noma: Muna iya ciyar da Jihar Sakkwato shinkafa -Abubakar Malami
Noman shinkafa a Jihar Sakkwato yana daya daga cikin noman da ke da tasiri. Sana’a ce da dubban mutane ke yin ta, kuma ba su san wata sana’a fiye da noman ta ba, domin da ita suke gudanar da rayuwarsu. Aminiya ta ziyarci wurin da ake noma shinkafa, wanda kusan shi ne jigo ga manoman, […]
Noman shinkafa a Jihar Sakkwato yana daya daga cikin noman da ke da tasiri. Sana’a ce da dubban mutane ke yin ta, kuma ba su san wata sana’a fiye da noman ta ba, domin da ita suke gudanar da rayuwarsu.
Aminiya ta ziyarci wurin da ake noma shinkafa, wanda kusan shi ne jigo ga manoman, aka tattauna da daya daga cikin manoman, kasancewar ba su da kungiya, ya yi bayani kan noman shinkafa da matsalolinsa.
Malam Abubakar Malami Gidan Maibugi ya kai shekara ashirin yana noman, ya bayyana nau’ukan shinkafa da yawa kamar ’yar futika da ’yar gwadargi da ’yar taro da bakin fari da zabuwa da mai adda da ’yar chana da sauransu.
Ya ce, “A nan Sakkwato mun fi noma jura da ’yar boto, in akwai yanayi na zurfin ruwa, amma inda ba yanayi na ruwa sosai mukan shuka taro da ’yar chana.”
Dangane da noman shinkafar, Malam Abubakar Malami ya ce abin da ya fi sauki shi ne a shirya ta sosai kamar yadda ake noman albasa, sai a watsa irinta. Yin haka zai taimaka mata, musamman in an samu karancin ruwa, ba za a samu matsala ba. Daga nan sai a sanya irin takin da ake da shi, a zuba maganin kwari, sai a rika kula da haki ana ciro, kuma a ba ta ruwa, yadda ya kamata. Wata shinkafar takan kai wata uku, wata kuma kasa da haka, sai a cire ta, don ta nuna.
A fannin matsaloli kuwa cewa ya yi akwai batun rashin taki da jari mai karfi, don noman shinkafa ba na talakan manomi ne ba. Duk manomin da ke son shinkafarsa ta inganta sai ya yi amfani da takin gida. “Shi takin gida karshe ne ga harkar noman shinkafa, matsalarshi dai yada haki; shi ko takin zamani yakan zaburar da shinkafa, amma ba ta da inganci. Ka ga wannan matsala ce da muke son mu kawar, ma’ana mu samu hayar inganta shinkafarmu, ta habaka nan take. Wannan kalubale ne ga masana aikin gona na Najeriya.
“Ina ganin da gwamnati za ta maida hankali gare mu, game da wannan lamari, to da za mu iya ciyar da Jihar Sakkwato shinkafa. Amma ina! A kullum za ka ji an ce za a taimaka wa talakawa; a yada a kafafen yada labarai, amma har yanzu! Mai yiwuwa dai ana taimaka wa masu noma da biro ne kawai”. Inji shi.
Shugaban masu sayar da shinkafa, Alhaji Umaru Kalambaina ya ce shinkafar da ake nomawa ba ta da inganci. Masaya sun fi son ta wani waje, don suna cewa ta nan ruwa take yi sosai, kuma ba ta da dadin aiki a wurin mata. Ko a wurin kudi ma suna da bambanci, ta nan tafi saukin kudi, kuma ba kowane dan kasuwa ke sayar da ita ba, don takan yi saurin lalacewa da hunhuna.
Malam Shehu Goronyo, jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar gona ta jiha, ya bayyana wa wakilinmu cewa, “Ai ko gwamnatin Jihar Sakkwato ta damu sosai wurin inganta noman shinkafa. Duk lokacin da za a raba taki mukan kara wa kananan hukumomin da ke noma shinkafa yawan taki fiye da wadanda ba su noma ta. Magana ce kawai, in har ba ka gode wa kokarin gwamnati ba, to ba za ka kushe ba, sai dai in kana da wani kulli cikinta.”