Noma shi ne tushen arzikin Najeriya
Noma tushen arziki, na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar. Wannan shi ne kirarin da na ta so na ji ana yi ga noma, wanda idan muka yi la’akari da kirarin nan na noma, za mu ga cewa noma wata dadaddar sana’a ce da muka gada tun a zamanin kaka da […]
Noma tushen arziki, na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar. Wannan shi ne kirarin da na ta so na ji ana yi ga noma, wanda idan muka yi la’akari da kirarin nan na noma, za mu ga cewa noma wata dadaddar sana’a ce da muka gada tun a zamanin kaka da kakanni.
Hakazalika, noma tushen arziki ne, ma’ana duk wani arziki da ya samu, to noma ne tushensa, wanda wannan a bayyane yake. Idan muka koma a tarihin kasar nan, an yi amfani da arzikin noma ne wajen samar da kudaden da aka soma hako ma’adanai, musamman man fetur da ake samarwa a kudancin kasar nan.
Hakika, dukkanin ci gaban kowace kasa ya rataya ne bisa samun hanyoyin samun kudaden shiga ga kasa ta fannoni da dama, kamar sarrafa abubuwa da za a fitar da su a wasu kasashe da kuma noma, da yake zama tushen arzikin kowace kasa.
A Najeriya, musamman a Arewa, Allah Ya hore mana albarkatun kasa daban-daban, musamman kasar noma, wadda za a iya amfani da wannan damar domin mayar da hankali kan fannin noma, domin kara samun kudaden shiga ga kasa.
Idan muka yi la’akari, duk yawancin abubuwan abinci da muke ci ko sha, akan noma su ne daga arewacin kasar nan. Alal misali, a jihohin arewacin kasar nan muke noma gero, dawa, shinkafa, wake, masara, gyada, alkama, inda wadannan abubuwan su ne kayan abincin da muka fi amfani da su, domin samar da abinci.
Baya ga wadannan, akwai kayan masarufi kamar kankana, tumatir, borkono, albasa, dankali, rake da ake sarrafawa a kudancin kasar nan, wadanda yawanci duk a arewacin kasar nan ake noma su. Bisa irin muhimmanci da kuma amfanin wadannan abubuwan, za ka samu akwai kamfanoni da damar gaske da suke sarrafa kayan masarufin da muke samarwa a Arewa. Abin mamaki, ba kamfani daya a arewacin kasar nan da ke sarrafa wadannan kayan masarufi, da ake nomawa a arewacin kasar nan.
Alal misali albasa, Jihar Sakkwato ta yi fice ciki da wajen kasar nan wajen noma albasa, kankana da tumatir amma ba kamfani daya da ke sarrafa kayan domin fitar da su, wanda galibi ’yan kasuwar wadannan abubuwan sukan tafka asara, a yayin daukar kayan daga arewacin kasar nan zuwa kudanci, sakamakon irin nisan da ke tsakanin arewacin kasar da kuma kudancin kasar nan.
A kasar nan, za ka je shagunan da ake sayar da kayan amfanin yau da kullum, amma abin mamaki za ka samu ruwan kankana a roba ko kuma tumatir din gwangwano, wanda kamfanonin da suke sarrafa tumatir din ba su kirguwa, wanda a arewa muke noma su, amma kanfanonin sukan ci amfanin kayan fiye da manomansu.
Hakazaliki, idan ana maganar noma, tabbas kiwo ma yakan zama hanyar noman, wanda shi ma kansa Arewa na taka rawar gani a wannan fannin, domiin a arewacin kasar nan ne muka fi kiwon dabbobi kamar awaki, shanu, rakuma, kaji, tumakai, da koyaushe za ka rika ganin manyan motoci na daukar dabbobi daga arewa zuwa kudancin kasar nan.
Sai dai kash! Duk wadannan abubuwan da muke da su, na arzikin kasa, manoma da kuma masu sana’ar kiwo na fuskantar kalubalen rashin kulawa da kuma rashin samun tallafin da za su bunkasa noman. Za ka samu gwamnati ta samar da iraruwa ga manoma da kuma taki domin amfanin manoma, sai ka samu daga karshe wadanda za su amfana da wannan tallafin, ba manoman gaske ba ne.
Saboda haka ya kamata gwamnati ta shigo cikin lamarin, kasancewar ana lokacin canji, ta hanyar yin tsayin daka na ganin an inganta fannin noma a arewacin kasar nan, da ma kasa baki daya. A kuma yi kokarin ganin an samar wa manoma tallafi na ingatattun iraruwa da kuma samar da taki ga manoma cikin lokaci, tare da tabbatar da cewa manoma na ainihi za su amfana da tallafin, tare da samar da kanfanonin da za su rika sarrafa kayan a arewacin kasar nan. Wannan zai sanya a jefi tsuntsu biyu da dutse daya, a samar da kudaden shiga ga kasa, a kuma samar wa matasa ayyukan yi.
Tabbas idan muka yi la’akari da irin wadannan albarkatun arzikin kasar noma da Allah (S.W.T) Ya ba mu a Arewa, ba karamar ni’ima ba ce a garemu da kuma kasarmu Najeriya. Da za a mayar da hankali a fannin, hakika kasar nan za ta yi gogayya da kasashen duniya wajen fitar da albarkartun noma da ake nomawa a kuma sarrafa a kasar nan. A bangaren ilimi kuwa, akwai bukatar bai wa dalibai masu nazarin aikin noma a jami’o’i da kuma makaratun aikin gona kulawa ta musamman tare da ba su tallafi da zai ba su kwarin gwiwar ci gaba da karatun fannin da za su iya fito da hanyoyi gudanar da noma cikin fasaha da zai tafi daidai da zamani.
A nan zan yi kira ga sauran jihohi da su yi koyi da Gwamnatin Jihar Sakkwato, na hada hannu da kamfanin tumatir na (Erisco) da zai kafa wajen sarrafa tumatir a jihar. Da kuma Gwamnatin Jihar Jigawa na hada hannu da kamfanin dangote, na soma noman shinkafa a jihar. Ya kamata sauran iihohin su ma su fito tare da hada hannu da sauran kamfanoni, na hada hannu da kamfanonin sarrafa albarkatun noma, domin kafawa a jihohin, doman samar da kudaden shiga da kuma rage yawan matasa marasa ayyukan yi.
dankaduna (09035522212) ya rubuto daga Sakkwato, [email protected] <mailto:[email protected]>;