Noma ya fi aikin gwamnati rufin asiri –Kwadom
Wani manomi a garin Kwadom da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, Malam Yahaya Ladan ya ce, sana’ar noma tafi aikin gwamnati rufin asiri a rayuwa. Malan Yahaya Ladan, wanda ya ce akalla ya kai shekara 40 yana harkar noman rani da na damina kuma ba abin da ba ya nomawa musamman a […]
Wani manomi a garin Kwadom da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, Malam Yahaya Ladan ya ce, sana’ar noma tafi aikin gwamnati rufin asiri a rayuwa.
Malan Yahaya Ladan, wanda ya ce akalla ya kai shekara 40 yana harkar noman rani da na damina kuma ba abin da ba ya nomawa musamman a lokacin rani irin yanzu.
Malam Ladan, ya yi bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a gonarsa ta latas da ke garin Kwadom inda ya ce, yanzu haka ya gama girbe masararsa ta rani yana aikin kayan lambu.
Ya ce, a lokacin rani kamar yanzu yana noma albasa da tumatir da latas har da masara.
Yahaya Ladan, ya ce, idan amfani ya yi kyau da damina yana noma buhu 50 na masara zuwa sama amma da rani bai kaiwa haka saboda maimakon ya zauna ba ya yin komai ne, shi ne yake yin na rani saboda duk kankantarsa idan ka gyara akwai albarka a cikinsa fiye da aikin gwamnati.
Ladan, ya ce, da rani yana noma buhu 50 zuwa 70 na albasa da tumatir saboda ana dibar tumatir ne yana kara haihuwa idan akwai damshi. Latas kuma idan aka deba yake rike musu dawainiyar gida na yau da kullum domin kullum haihuwa yake.
Sai ya ce, kalubalen da suka rika fuskanta a bangaren noman rani shi ne na samun ruwa kafin su gano tona rijiyar burtsatse.
Ya yi kira ga gwamnati ta taimaka musu da taki a farashi mai sauki da maganin kwari domin a cewarsa suna da matsalar kwari.
Ya ce ana faduwa a noma amma idan mutum ya san yadda zai yi noma ta yadda zai samu ribar sa ta fi faduwar yawa.
Ya ce, sun tashi sun ga ana noman ne a gidansu, shi ya sa suka rungumi harkar gadan-gadan inda ta kai ga ko aikin gwamnati aka ba shi ba zai yi ba saboda ribar da yake samu a noman.