Noma zai iya maye gurbin fetur a Najeriya -danmaliki

Wani babban manomin rani Alhaji Abubakar Musa danmalikin Kabi ya ce manoman kasar nan za su iya samar da abinci wadatacce da Najeriya take bukata, idan har gwamnatocin tarayya da na Jihohi suka ba su cikakken goyon baya ta fannin kayan aiki. Ya yi wannan bayani ne a yayin tattaunawarsu da wakilinmu, inda ya kara […]

Noma zai iya maye gurbin fetur a Najeriya -danmaliki

Wani babban manomin rani Alhaji Abubakar Musa danmalikin Kabi ya ce manoman kasar nan za su iya samar da abinci wadatacce da Najeriya take bukata, idan har gwamnatocin tarayya da na Jihohi suka ba su cikakken goyon baya ta fannin kayan aiki.

Ya yi wannan bayani ne a yayin tattaunawarsu da wakilinmu, inda ya kara da cewa akwai kasar noma mai dausayi a kowane bangare na kasar nan kuma su kansu manoman suna da kwarewa kan aikin noma, amma rashin yin wani tsari ingantacce tun da farko ya sanya ake samun koma-baya ta fuskar noma a kasar nan.

Haka kuma ya sanar da cewa lokaci ya yi da za a kara samo wasu hanyoyi na samun kudaden shiga a kasar nan, musamman ganin cewa man fetur din da ake dogara da shi yana samun koma baya ta fuskar farashi a kasuwar duniya, kamar yadda abin yake tafiya a halin yanzu.

Manomin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohin kasar nan da su bullo da wani tsari mai gamsarwa ta yadda manoma za su samu cikakken tallafi domin bunkasa noma, musamman ganin cewa kasashen da suka bunkasa ta fannin noma sun zamo abin misali ta fannin tattalin arziki da kuma batun fitar da kayan amfanin gona zuwa wasu kasashe na duniya.

Sai ya yi fatan cewa daga wannan shekara gwamnatocin kasar nan za su kara daukar fannin noma da matukar muhimmanci tare da yin tsari mai kyau wajen ba manoma tallafi na kayan aikin gona, kamar takin zamani da irin shukawa da kuma magungunan feshi, tun kafin faduwar damina, kamar yadda ake yi a kasashen da suka cigaba ta fuskar noma. 

Ya ce ya kamata gwamnati ta kara inganta ayyukan malaman gona, wadanda sune suke tare da manoma rani da damina suna ba su shawarwari, inda kuma daga karshe ya bayyana gamsuwarsa da yadda gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnatin Jihar Kebbi suke daukar matakai na ciyar da kasar nan gaba ta fannin noma.