Noman dankalin Turawa na da riba in – Sabo Ibrahim
Wani manomi a Karamar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina Alhaji Sabo Ibrahim ya ce, noman dankalin Turawa na da riba muddin manomi zai samu kayan da yake bukata. Alhaji Sabo Ibrahim na Unguwar Kanawa da ke Bakori ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya, inda ya ce, duk da cewa noman dankalin Turawa […]
Wani manomi a Karamar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina Alhaji Sabo Ibrahim ya ce, noman dankalin Turawa na da riba muddin manomi zai samu kayan da yake bukata.
Alhaji Sabo Ibrahim na Unguwar Kanawa da ke Bakori ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya, inda ya ce, duk da cewa noman dankalin Turawa bai yawaita ba a jihar idan aka kwatanta da wasu jihohin; duk da haka yakan noma akalla kadada hudu na dankalin Turawan.
Game da tsadar noma Alhaji Sabo ya ce“Noma zai yi tsada ne in har ba a samun tallafi daga gwamnati, wato rashin samun iri mai kyau da takin zamani da injinan ban-ruwa da sauransu. Sannan ga batun leburori, amma duk da wannan cikin ikon Allah bai hana ni noma wannan adadi na gona. Kuma a duk lokuta biyu rani da damina ina noma dankalin Turawan kuma ina ganin ribar abin. Inda kawai za a samu matsala shi ne idan ba a samu tallafi daga gwamanti
“Kuma ina so jama’a su sani, a yanzu muna iya noma dankalin Turawa da za mu ciyar da wasu jihohin ba Jihar Katsina kadai ba, kuma za a samu saukin farashinsa da azumi lokacin da yake yin tashin gwauron zabo,” inji shi.
Da ya juya kan noman damina, Alhaji Sabo ya ce, matsalar duk iri daya ce da noman ranin duk da cewa ya fi ba noman dankalin fifik a noman daminar. Sai dai kuma manomin ya koka kan rashin samun tallafi daga gwamnati a sashen noman dankalin Turawan. Saboda haka, ya yi kira ga gwamnati da kungiyoyin manoma da ke jihar su shigo su bayar da gudunmawarsu wajen noman dankalin Turawa a jihar. Ya ce akwai dimbin ribar da ake samu a nomansa. “A yanzu a nan Kudancin Jiha da Arewar babu irin kayan amfanin gonar da ba mu nomawa a rani da damana, kuma kullum muna kokarin tafiya da zamani. Insha Allahu, nan gaba sai Jihar Katsina ta sake maido tarihinta ta fuskar noma, amma sai tare da taimakon gwamnati,” inji shi.
In dai za a iya tunawa, Kungiyar Inuwar Manoma a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina Alhaji Ya’u Gwajogwajo ta ce, za ta inganta noman dankalin Turawa da sauran nau’o’in kayan gona da ba a noma su a jihar. Sannan kungiyar za ta yi ruwa-da-tsaki don ganin ta nemo wa manoman duk wata gudunmawa don ganin noma ya inganta a jihar.