Noman karas alheri ne – Manomi
Buhari Muhammad, wanda yake noman rani a rafin Kubanni a gonar karas din da ya shuka tare da ’ya’yansa, ya yi bayani yadda ake noman karas da irin amfanin da yake samu a noman ranin. Ya ce: “Da farko dai za a yi kaftu sannan a yi kwami; to bayan ban-ruwa sai a yafa irin […]
Buhari Muhammad, wanda yake noman rani a rafin Kubanni a gonar karas din da ya shuka tare da ’ya’yansa, ya yi bayani yadda ake noman karas da irin amfanin da yake samu a noman ranin.
Ya ce: “Da farko dai za a yi kaftu sannan a yi kwami; to bayan ban-ruwa sai a yafa irin a cikin kwamin, bayan kwana biyar za ka ga duk ya tsira, to daga nan sai a sa taki sannan a yi masa ban- ruwa daga nan sai a yi masa ciro kamar yadda ka ga muna yi yanzu, kuma shi wajen ciron ba a yin garaje domin yanzu ka ga yadda muke bi muna ciro daya bayan daya ni da yarana. Kuma daga nan sai a yi masa feshin maganin darba, ko tsutsa domin kada su tauye ta.”
Buhari Muhammad ya kara da cewa, “Noman karas yana daukar tsawon wata uku kafin a fara ci. To kamar yadda ka sani ne duk abin da ya shafi kayan gwari ba ya da tsayayyen farashi, domin ka ga dai a karshen damina lokacin da ake cikin kakan amfanin gona to shi a lokacin ake kamfarsa, kuma a lokacin aka fi samun kudi a kusan dukkan nau’o’in kayan da suka fi zuwa da rani.”
Ya ci gaba da cewa: “Noman rani shi ne sana’ar da na fi ba da karfi a kai a tsawon lokaci domin kamar gadonsa na yi a gidanmu domin ba wata sana’ar da ta wuce noma a gidanmu, sai saye da sayarwa; shi ma na amfanin kayan da aka fi nomawa ne da rani, domin haka na taso na ga shi ne harkat gidanmu na duk wani nau’in noman kayan rani.”
Ya ce duk wani abu da ya mallaka kamar aure da gida da abin hawa da sana’ar noman rani Allah Ya sa ya samu kuma yana alfahari da noman rani.
Ya bayyana cewa, bai taba samun wani tallafi daga wajen wani ko hukuma ba, kuma ko da shawara ce kan noman ranin da yake yi.