Noman masara yana da tasiri ga tattalin arzikin kasa – Bello Annur
Alhaji Bello Abubakar Annur, shi ne Shugaban Kungiyar Manoman Masara ta Kasa (MAAN), ya shahara wajen noman masara a ciki da wajen kasar nan inda wannan ya sa ya sami digirin girmamawa a wata jami’ar kasar waje. Aminiya ta zanta da shi kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da noman masara a Najeriya. Mene […]
Alhaji Bello Abubakar Annur, shi ne Shugaban Kungiyar Manoman Masara ta Kasa (MAAN), ya shahara wajen noman masara a ciki da wajen kasar nan inda wannan ya sa ya sami digirin girmamawa a wata jami’ar kasar waje. Aminiya ta zanta da shi kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da noman masara a Najeriya.
Mene ne tasirin noman masara ga tattalin arziki?
Masara tana daya daga cikin kayan abinci mafiya muhimmanci a kasar nan, dalili kuwa masarar da muke nomawa a kasar nan kashi 60 cikin 100 gidajen kaji suke amfani da ita. Ka ga ashe masara tana da matukar muhimmanci domin kamfanonin abincin kaji suke saye su sarrafa ta sannan masu noman kaji su saya domin kajinsu. Ka ga ashe noman masara na da alaka da samar da kaji da kwai a kasa sannan gwamnatoci a dukkan matakai suna karbar haraji, ke nan noman masara yana da tasiri ga tattalin arziki.
Bayan abincin kaji, ko akwai wata hanya da ake sarrafa masara?
Akwai masana’antu masu yawa da suke amfani da masara baya ga na abincin kaji, akwai kamfanin abincin yara da kamfanonin magani. Domin a cikin masara akwai sinadaran da ake cire su da masu sarrafa magani ke amfani da su waje hada magunguna. Sannan ana sarrafa totuwar masara a wasu kasashen domin samar da wutar lantarki.
Akwai kamfanin da ya tuntube mu kan wannan batu na totuwar masara, saboda haka noman masara na da matukar tasiri ga tattalin arzikin kasa idan aka dubi yadda ake sarrafa ta. Wadansu sun dauka masara tuwo kawai ake yi da ita, alhali ana sarrafa ta ta hanyoyi da yawa. Ta hanyar noman masara kadai gwamnati za ta bunkasa tattalin arzikinta.
An samu ambaliyar ruwa a wasu jihohi wace asara ta jawo muku?
Gaskiya bana an samu damina mai albarka domin ta yi abin da ake cewa harshe, da farko masana sun fitar da sanarwar cewa za a samu daukewar ruwa da wuri sai kuma aka samu akasin haka. To a wani bangare an samu asara mai yawa musamman ga wadanda suka yi shuka da wuri, amma ga wadnda suka yi shuka daga baya sun samu amfani mai yawa. Wadansu sun riga sun girbi amfanin yana gona sai ruwa ya lalata musu, wadansu kuma ruwa ne ya shafe gonakin nasu ya jawo musu asara mai yawa. Hakika wannan asara ta shafi manoman masara da yawa sai dai muna fata Allah Ya mayar wa wadanda suka yi asara da alheri.
A halin yanzu muna tattara rahoto a kan yawan kudin da manoma suka yi asara a bana, nan da wani lokaci za mu sanar da adadin.
Jihohi nawa wannan asara ta shafa?
A bisa ga kididdigar da muka samu ta nuna cewa akwai jihohi takwas wadanda asara ta fi shafa da suka hada daga Kudu da nan Arewa. Daga ciki akwai jihohin Borno da Jigawa da Kano da Bayelsa da Kogi da Oyo da Kuros Riba da kuma Katsina. Akwai wasu jihohin da suka samu wannan asara amma inda ta fi kamari su ne wadannan jihohi takwas.
Kungiyarku ta ba manoma bashi ga shi an samu asara yaya za a yi da su?
To muna hulda da wani kamfanin inshora domin duba yadda za a bullo wa lamarin, kuma da zarar an kamalla kiyasin asarar za mu duba yadda za a rage wa manowa wannan radadi da suke ciki. Abu ne da aka sani idan bankin manoma zai ba ka bashi sai ya tabbatar kana da inshora ko da irin haka za ta kasance, mu ma kafin su karbi wannan rance mun yi irin wannan tanadi don haka muna aiki a kai.
Ko rufe iyakokin kasa ya yi tasiri ga noman masara?
Rufe iyakokin kasa ya samar da gagarumar nasara ga noman masara domin tuni muka fito muka yaba wa gwamnati kan wannan mataki da ta dauka domin a da farashin masara ya karye warwas sakamakon shigo da ita barkatai da ake yi. Amma yanzu manoman masara suna samun nasara a harkarsu ta noma. Kuma wannan abin da gwamnati ta yi kamar don manoma masara aka yi, domin akwai mutane marasa kishi masu shigo da masara daga kasashen ketare inda wannan ya sa masu noman masara suke tafka asara. A bara ana sayen buhun taki a kan Naira dubu tara kuma buhun masarar ana sayar da shi a kan Naira dubu biyar, amma daga lokacin da aka rufe kan iyakokin kasa yanzu manoma suna iya noma ta kuma su sayar su ci riba domin yanzu buhunta yana kaiwa Naira dubu takwas zuwa dubu tara ka ga sai hamdala.
A halin yanzu muna samun kamfanoni daga waje suna zuwa wajen kungiyoyi irin namu domin ganin an dama da su wajen inganta aikin gona.
Wace barazana manoma masara suke fuskanta?
Babbar barazanar da muke fuskanta ita ce mutanen da suke shigo da masara suna bibiyar gwamnati da ’yan siyasa domin ganin an ba su dama su ci gaba da shigo da masara suna yi wa gwamnati karya cewa ba ma iya noma masarar da ake bukata a kasa. Wannan karya ce kuma muna kira ga gwamnati ta yi watsi da wadannan mutane wadanda ba su da kishin kasa, domin sun saba da barna a kasa.
Kuma muna shirin aike wa gwamnati rahoton yawan masarar da ake nomawa a kasar nan domin har yanzu muna da ragowar masarar da muka noma bara a cikin rumbunan ajiyarmu amma ba su zo sun saya ba. Don haka muna kiran gwamnati ta yi watsi da wadannan mutane, kuma duk lokacin da suka zo wajen gwamnati to muna kiran gwamnati cewa su kira wadannan mutane mu zauna tare domin fayyace gaskiya.
Mene ne babban burin wannan kungiya taku?
Muna so mu ga noman masara ya bunkasa a kasar nan, bayan mun wadata kasa da masara ya zama muna samar wa masana’antunmu masarar da suke bukata sannan mu fitar da ita zuwa kasashen waje domin samar wa kasa haraji da kudaden musaya. Sannan mun dauki matakai a kan haka, abin da ake bukata kafin mu fara fitar da masara zuwa kasashen waje akwai wasu sinadarai da ake so masararmu ta zama tana da su wadanda da su ne duniya za ta yarda ta karbi masararmu. Wannan dalili ya sa muka shiga yarjejeniya da kamfanoni da kuma Gwamnatin Tarayya domin samar da wannan sinadari, wanda da shi ne noman masara zai inganta kuma duniya za ta karbe ta. Sannan yana daga cikin burinmu mu samar da wani yanayi da manomanmu za su rika amfani da injinan zamani wajen noman masara kuma a yanzu haka mun fara samar musu da wadannan kayan aiki.
Mene ne kiranka ga manoma masara?
Ina kira ga manoma su kasance masu shiri a kullum domin tunkarar aikin da ke gabansu, sannan manoma su kasance suna yin tattali kada ya zama daga ka yi girbi sai ka sa abin da ka noma a gaba ka cinye idan damina ta fadi mutum ya fara kame-kame. Ya kansance manoma suna da kula da kuma yi wa kansu tanadi.
Sannan kirana ga manoma masu karbar bashi lallai su yi wa kansu abin da ya dace wajen biyan bashi, domin biyan bashi yana daga cikin kamala, sai kun biya bashin nan sannan za a ba wadansu don haka mu daure mu rika biyan bashin da muka karba a kan lokaci.