Noman rani: Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa manoman Kebbi da Zamfara

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar samar da jigogin ban-ruwan na zamani ga noman rani a jihohin Kebbi da Zamfara domin kara inganta noman, bayan kananan rijiyoyin burtsatse da ake amfani da su. Daraktan Noman Rani da Magudanun Ruwa a Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya, Mista Elijah Aderibegbe ya ce aiwatar da […]

Noman rani: Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa manoman Kebbi da Zamfara

Irin jigogin ban-ruwa na zamani da aka samar a wata gona

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar samar da jigogin ban-ruwan na zamani ga noman rani a jihohin Kebbi da Zamfara domin kara inganta noman, bayan kananan rijiyoyin burtsatse da ake amfani da su.

Daraktan Noman Rani da Magudanun Ruwa a Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya, Mista Elijah Aderibegbe ya ce aiwatar da tsarin wani bangare ne na yunkurin da ake yi na karfafa noman rani a kasar nan.

Kuma ya ce abu ne da zai kara habaka aikin noma da samar da wadataccen abinci ga kasa.

Tsarin jigogin shida za a yi su a Jihar Kebbi, uku za a kai su Zamfara, an yi haka ne domin a zaburar da manoma kan aikin noma na zahiri a Arewa ta Yamma ganin yankin ya yi fice a harkar noma.

Ma’aikatar Ruwa ta mika jigogin ban ruwan guda tara ga Hukumar Kogin Rima da ke Jihar Sakkwato. Kuma ana sa ran samar da jigogin ya kara habaka aikin noman rani da kawar da barnar ruwa a lokacin ban-ruwan noman rani.

Kawar da almubazaranci da ruwa abu ne da duniya ta sanya a gaba kuma an samar da shi  ne bisa muhimmanci ga harkar noma don ba a son amfanin gona ya samu karancin ruwa.

Bankin Duniya ya fitar da kididdiga cewa aikin noma ke lakume kashi 70 ckin 100 na ruwan da ke yawo a duniya. Sannan noman rani bai samar da abincin da ake bukata. Sun kara da cewa “A duniya gaba daya akwai sama da kadada miliyan 330 da ake noman rani, kuma a shimfidaddiyar kasa da ake da ita a duniya kashi 20 cikin 100 nata noman rani ake yi amma a abincin da ake samarwa a duniya kashi 40 kawai yake samarwa.”

Jihar Kebbi tana daya daga cikin jihohin da suka samu jigogin, da yawan manoma sun shiga cikin harkar noman rani, amma suna korafi kan yadda suke shan bakar wahala in za su yi ban-ruwa saboda karancin ruwa a madatsu.

Alhaji Kabiru wani babban manomi mai gonaki kadada 60 ya ce yana amfani da injunan ban-ruwa 52 da suke bai wa shukarsa ruwa. A cewarsa injunan nasa kullum suna amfani da fetur lita 70,000, inda ya koka da hakan. “Mafi yawan ribar da muke samu tana tafiya ne ga mai da takin zamani da masu yi mana aiki, hakan ne ke sanya shinkafar da muke nomawa take yin tsada a kasuwa,” inji shi.

Yana ganin daga fara noman shinkafa zuwa girbe ta akalla yana kashe Naira miliyan uku zuwa uku da rabi.

“A lokacin da ruwan sama ya dauke dole ne ka yi ban-ruwa sau biyu domin shuka ta yi kyau a wannan yanayi kuwa ina kashe Naira miliyan hudu ko hudu da rabi ya danganta da buhu 1000 ko 1,500.

Alhaji Kabir ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gyara dam da suke amfani da shi. Fadamarmu ce ta taso daga Bunza zuwa Bagudo akalla ta kai kilomita 200 kuma duk wadanda ke aiki a wurin da inji suke yi.

Ya yaba da sababbin jigogin ban-ruwa da Gwamnatin Tarayya ta samar, “Amma amfaninsa na ga yadda Gwamnatin Tarayya ta samar da shi da sauki ga manoma. Kuma ta rika kula da shi da samar da shi a ko’ina.

Tunda lamarin ya koma na zamani akwai bukatar canja wa kananan manomanmu tsarin noma, wannan sabon tsari abin yabawa ne da fatar hakan zai taimaki manoma a Kebbi. Sakataren Manoman Jihar Kebbi Alhaji Mohammad Idris Birnin Kebbi ya ce ban-ruwa ne matsalar manoman jihar. “Wannan shiri zai taimaki manoman Kebbi har su iya ciyar da kasa da abinci,” inji shi.Ya shawarci gwamnatin ta fadada shirin ya kai dukkan kananan hukumomi 20 na jihar kuma a shigo da sarakunan gargajiya da manoman gaskiya domin samun nasara.

Manoman sun kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta tabbatar ta shigo da kanana da manyan manoma cikin shirin.

Ya ce Hukumar Abincin ta Majalisar Dinkin Duniya (FOA) ta ce jikin duniya ya yi sanyi game da samun wadataccen abinci ganin yadda ake samun karancin ruwa.  Ta ce ana bukatar ruwa mai yawa ganin yadda al’umma ke karuwa kuma suna bukatar abinci. “Sha’anin noma na fuskantar manyan kalubale daga yanzu zuwa 2050 kan yadda za a iya ciyar da mutum biliyan tara, ana bukatar karin ruwa kafin a samu karin abinci a kasashe da kashi 60 kan wanda ake da shi yanzu. Samar da ruwan a yanzu yana kashi 25 zuwa 40,” inji shi.

Ya ce Hukumar FOA ta ce “Wannan sauyin ana tsammaninsa ya zo daga wurin manoma saboda su ne suka fi amfani da ruwa.”

Daraktan Noman Ranin ya bayyana yadda yake kallon shirin na jigogin ban-ruwan da cewa “Za su taimaka sosai, kuma wadanda suka samu za su ci amfaninsu wajen samar da wadattacen abinci a kasa.”