Noman rani: ‘Mutanenmu sun rage zuwa cirani’
Shugaban Karamar Hukumar Kudan a Jihar Kaduna, Alhaji Shu’aibu Bawa Jaja ya ce gyaran da Karamar Hukumar ta yi wa madatsar ruwa ta Garu ya rage kwararar al’ummar yankin zuwa cirani. Bawa Jaja ya ce kimanin manoma dubu uku ne ke amfana da madatsar bayan an yashe ta na zurfin mita biyar, shekara 40 bayan […]
Shugaban Karamar Hukumar Kudan a Jihar Kaduna, Alhaji Shu’aibu Bawa Jaja ya ce gyaran da Karamar Hukumar ta yi wa madatsar ruwa ta Garu ya rage kwararar al’ummar yankin zuwa cirani.
Bawa Jaja ya ce kimanin manoma dubu uku ne ke amfana da madatsar bayan an yashe ta na zurfin mita biyar, shekara 40 bayan an gina ta domin noman rani.
“Don haka muka yanke shawarar gina wa al’ummarmu kasuwa ta zamani don bunkasa harkar kasuwancin amfanin gona da inganta tattalin arzikin al’ummar karamar hukumarmu”, inji shi.
Ya koka da cewa Kudan ce kan gaba a noman rake a Jihar, amma kasancewar Makarfi cibiyar kasuwancinsa ya sa Makarfin ta fi ta shahara da harkar raken.
Shugaban Karamar Hukumar ya ce manoman Kudan ne ke noma da kusan kashi 65 na kayan marmari na noman rani da ake samarwa a Jihar Kaduna.
A cewarsa, ko babbar kasuwar Mike 12 da ta shahara wajen kasuwancin kayan gwari da na marmari a Jihar Legas, mutanen Kudan ne suka kafa ta shekaru da dama da suka gabata.