Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum
Kafa manyan gonakin noman rani na buƙatar jajircewa daga gwamnoni.
![Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2022/12/Gwamnan-Bono-Babagana-Zulum.jpg)
Gwamnan Borno, Babagana Zulum
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jaddada buƙatar samar da manyan gonakin gudanar da noman rani domin yaki da matsalar karancin abinci a Yankin Tafkin Chadi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin taron Gwamnonin Tafkin Chadi da aka gudanar makon da ya gabatar a garin Maiduguri fadar Jihar Borno karo na biyar, inda ya jadadda cewar, Allah SWT ya azurta wannan Yanki na Tafkin Chadi da dimbin filayen noma wanda idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, na iya ba da gudummawa sosai wajen samar da abinci a yankin har ma da yankuna makwabta.
Zulum ya bayyana muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnonin yankin da abokan haɗin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya domin kafa gonakin noman rani masu inganci.
Ya yi nuni da cewa dogaro da noman damina kadai ba zai dore ba, saboda karuwar al’ummar yankin, wanda ala tilas sai an hada da noman rani.
Zulum ya kuma jaddada bukatar yin bincike kan amfanin gona masu jure yanayi don tabbatar da isasshen abinci da wadatar abinci ga al’ummar wannan yanki.
Ya ba da shawarar cewa, shirin noman ranin zai iya tallafa wa ci gaban kiwon dabbobi, yadda za a samu wadataccen nama da kuma nono a yankin.
A cewar gwamnan, “kafa manyan gonakin noman rani na buƙatar jajircewa daga gwamnoni da abokan tarayya da gwamnatocin kasashenmu don ganin mun cim ma manufar hakan a kan lokaci, yadda al’ummomin za su amfana”, in ji shi.
Ya kuma jaddada cewa, “gabar Tafkin Chadi na samar da wadataccen ruwa, kuma ana iya haka rijiyoyi da sanya bututun tura ruwa inda ruwan ya yi ƙaranci don al’ummar wuraren su amfana.”