Nonon shanu na inganta sha’awa
Assalamu Alaikum wa rahma-tullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, musamman wadanda suka […]
Assalamu Alaikum wa rahma-tullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.
Tambaya ta 13: Don Allah ina so ku yi mini bayanin abin da ya kamata in rika yi wa mijina a duk lokacin da muke tare, kuma ya zan yi in gane ina gamsar da maigidana, kuma don Allah mene ne amfanin shan nonon shanu?
– Ummy Zamfara
Amsa: ’Yar uwa Ummi, ki sani, kowane namiji bukatunsa daban da na waninsa: wani yanga yake so, wani kwarkwasa, wani tsabta, wani kwalliya, wani natsuwa da rashin kwaramniya, wani ma jan aji yake so a yi rika yi masa, wani kuma shagwaba, wani kissa da kisisina, wani so yake ki mai da shi kamar dan lele, ki yi ta ji da shi kina tarairayarsa; haka kuma abin yake ko a wajen tarayyar ibadar aure.
Don haka ke ya kamata kisa ido ki lura da yanayin mijinki, ki fahimci me ya fi so, me ya fi saurin sanya shi farin ciki? Duk abin da kika lura shi ne, sai ki rika yi masa. Wajen ibadar aure kuma ki sake jikinki ki ba shi cikakken hadin kai, kuma ki ba da taki gudunmuwar wajen ayyukan gabatarwar ibadar auren. Kuma za ki iya tambayarsa kai tsaye, duk abin da ya sanar miki to sai ki rika yi masa shi. Nonon shanu abinci ne mai kyawu kuma mai inganta lafiyar jiki, wannan kuwa har da lafiyar ma’aikatar sha’awa, sannan nonon shanu yana samar da lema ga ‘yanmatancin mace kuma yana dauke da kyawawan sinadarai masu inganta lafiyar ma’aikatar sha’awa.
Tambaya ta 14: Mafi yawan lokuta uwargida kan bata ni da fitsari lokacin ibadar aure, kuma ko ta je ta yi fitsarin kafin mu kwanta sai hakan ta faru; mene ne mafita?
– M. A. Bash.
Amsa: kasancewar mafitsara na makwabtaka da kofar ‘yanmatanci, kuma belin ‘yanmatanci shi ma gab da gab yake da kofar fitar fitsari, sannan kuma jijiyoyin da ke kula da rufewa da budewar kofar fitar fitsari shimfide suke a karkashin ‘yanmatancin mace, ga shi kuma su ne masu dawaniya lokacin ibadar aure, wannan ne ya sa dawainiyar ibadar aure ke haifar da zubowar fitsari ga wasu matan musamman wadanda jijiyoyin ‘yanmatancinsu sun yi rauni a dalilin yawan haihuwa ko a dalilin wata matsala ta daban.
Idan jijiyoyin mafitsara sun yi rauni sosai, motsi kadan, kamar atishawa ko tari na iya sa fitsari ya zubo. Mata masu irin wannan matsala kan ji fitsarin ne da zarar an fara gabatar da ibadar auren, wasu kuma sai a lokacin da suka kai ga cim ma biyan bukatar sha’awarsu. Wannan ke sa wasu suna danne sha’awarsu don dai tsoron zubowar fitsarin.
Abu na farko shi ne sai a je a ga likita a yi masa bayani, bayan ‘yan gwaje-gwaje za a samu maganin da zai warkar da matsalar in sha Allah. Sannan uwargida ta daure ta rika yin samfurin motsa jijiyoyin al’aura na kegel, wanda shi zai gyara tare da inganta jijiyoyin mafitsararta. Hanya mafi sauki ita ce ta je asibitin masu yoyon fitsari, ana samun ‘yar na’urar kegel din sai ta rika yi kullum ba fashi har sai ta ga bayan wannan matsala.
Sannan sai ta daina shan abubuwa masu yawan sa fitsari irinsu ganyen shayi da nescafe da goro da magungunan Hausa ko na Bature masu dauke da sinadarin caffeine. Sannan sai ta rage shan ruwa ko wani abu mai ruwa sa’o’i uku kafin lokacin ibadar auren.
Tambaya ta 16: Wane irin magani ya kamaci mazan da ba su da kuzarin sha’awa su dinga amfani da shi.
– I. C. Tsafe.
Amsa: Ba wani magani da ya wuce lafiyayyen abinci da ‘ya’yan itace da ganyayyaki.
Tambaya ta 17: Don Allah muna so a fada mana sunan kalar turaren da za mu samu domin sanyawa a baki da wurin da za mu same shi.
– S.A Garko.
Amsa: Sunanshi “Breath freshener” kuma ana samun sa a shagunan da ake sayar da kayan shafawa da na gyaran jiki.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.